HOTUNA: Ziyarar Osinbajo a Kano

A Talatar da ta gabata Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Kano. Osinbajo ya ziyarci Kano ne don halartar taron Lakcar Tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardauna wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta saba shiryawa duk shekara.