Muhyi Magaji Rimingado ya shaƙi iskar ‘yanci

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Bayan tataɓurza da aka samu tsakanin tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado da lauyoyinsa da kuma lauyoyin gwamnati, daga ƙarshe dai an cimma matsaya inda aka bayar da Belinsa,

‘Yan sanda ne dai suka gurfanar da Muhuyi a gaban kotu mai lamba 56 a ƙarƙashin mai Shari’a Aminu Gabari bayan da suka kamo shi a Abuja bayan da suke masa zargin gabatar da takardun lafiya na bogi ga majalisar dokokin Kano, tun a wancan lokacin anyi ta musayar yawu ta bayan fage, sannan har karo biyu ‘yan sanda na yunƙurin kama shi har gida, amma hakan bai yiwuwa ba.

A yayin zaman kotun na jiya dai an gabatar wa da Muhuyi tuhumar da ake yi masa abinda ya musanta nan take daga nan ne lauyan gwamnati ya nemi a dage shari’ar har zuwa ranar 14 ga watan gobe domin su gabatar da hujjoji su.

To amma bayan dawowa hutun awannin biyu ne kotu ta amince da buƙatar lauyan Muhuyi na bayar da belinsa a bisa sharuɗɗan zai ajiye kuɗi naira dubu ɗari biyar tare da mutane biyu da za su tsaya masa waɗanda suka haɗa ɗan uwa ko uba a wajensa da kuma babban limamin masallacin Juma’a na Sharaɗa ko Ja’en.

Alƙalin, ya kuma umarci wanda ake ƙara da ya miƙa takardun tafiye-tafiyensa ga kotun.

Haka kuma an hana Muhyi yin magana a kafafen yaɗa labarai ko a kafafen sada zumunta, har zuwa huɗu ga watan Mayu mai kamawa don a cigaba da shari’ar.

Rahotanni sun nuna cewa Muhyi Magaji an sammameshi ya koma gida cikin ƙoshin lafiya.

By Editor