Har yanzu mata suna baya wajen samun madafun iko a Nijeriya – NBS

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, ta bayyana cewa har yanzu an bar mata a baya a Nijeriya wajen samun madafun iko, idan aka kwatanta su da maza a ƙasar.

Wannan na ƙunshe ne a wani rahoto da ya fita ranar Lahadi a Abuja daga Kundin Ƙididdigar Jinsi na Watanni uku-uku, na wata ukun farko a 2022.

Kundin rahoton ya maida hankali ne a kan wasu lamura uku da su ka haɗa da, mulki, madafar iko, lafiya, ƙididdigar al’umma da kuma ilimi.

A cewar rahoton, ƙididdiga ta nuna cewa kashen mata da su ke fitowa a matsayin abokan takarar shugabancin ƙasa daga 2019 zuwa 2022 kashi 0 ne cikin 100,  yayin da na maza kuma 100 ne bisa 100.

Rahoton ya ƙara da cewa adadin mata 6 ne su ka tsaya takarar shugaban ƙasa a 2019, inda maza kuma 67 ne.

Sai kuma ya ƙara da bayyana cewa adadin mata 26 ne su ka tsaya a matsayin abokan takara, a maimakon 52 daga ɓangaren maza. 

Hakazalika, rahoton ya ce mata 80 ne su ka fito takararar gwamna a zaɓen 2019, inda maza kuma su  984 ne, inda mata 271 su ka zama abokan takarar gwamna, su kuma maza su 789 ne. 

Rahotannin ya kuma yi nuni da ɓangarori da dama da muƙaman maza su ka ninninka na mata a faɗin ƙasar nan.

By Editor