’Yan sanda sun daƙile yunƙurin IPOB na ƙona gidan rediyo a Anambara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Anambara ta tabbatar da wani hari da aka kai wa gidan rediyon jihar Anambra, ABS, da sanyin safiyar Litinin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambara, DSP Toochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin.

Ikenga ya ce waɗanda ake zargin ba su samu nasarar kaiwa ga ɗakin watsa shirye-shirye, amma kuma sun yi nasarar ƙona wasu motoci guda biyu na tashar.

Ya ce, biyo bayan wani kiraye-kirayen da aka yi 30 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 4:30 na safiya, na wani hari da a ka kai a gidan rediyon jihar Anambara da ke Idemili ta Arewa, tawagar ‘yan sanda da ke sintiri ta mayar da martani cikin gaggawa.

“Amma kuma mun hana ɓata-garin yin kai harin a kan ginin. Abin takaici, motoci biyu na aiki mallakar tashar ne abin ya shafa. Ba a rasa rai ba. A halin yanzu, an killace tashar kuma ana ci gaba da gudanar da aiki a yankin,” inji shi.

By Editor