CMG ya ƙaddamar da aikin kafofin watsa labarai na kare muhalli na Sin da Afirka

Spread the love

Daga CMG HAUSA

A yayin bikin “Ranar Muhalli ta Duniya” da aka yi a yau Lahadi, an kaddamar da “Aikin kafofin watsa labarai na kare muhalli na Sin da Afirka” a hukumance, wanda sashen babban gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin wato CMG dake nahiyar Afirka ya ƙaddamar a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

A yayin bikin ƙaddamar da aikin, CMG da muhimman kafofin watsa labaru na wasu ƙasashen Afirka da dama, sun gabatar da shawarar “Yin murya domin muhallin halittu” tare, inda aka yi kira ga kafofin watsa labaru na ƙasar Sin da na Afirka da su haɗa ƙarfi don inganta mu’amala da koyi da juna a tsakanin jama’a kan ra’ayoyi da ayyukan kare muhalli.

Wakilai sama da 30 daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar UNEP, UNDP, UNICEF, da WWF, wakilan shugabannin siyasa daga ƙasashen Afirka, jami’an hukumomin kare muhalli, da wakilan manyan kafofin yada labarai daga ƙasashen Afirka da dama ne suka halarci bikin ƙaddamar da aikin.

Susan Gardner, darektar sashen kula da muhalli na UNEP, ta ce kafafen yada labarai na iya “jawo hankalin jama’a kan al’amurran muhalli da aka yi watsi da su, tare da gabatar da hujjoji ba tare da nuna banbanci ba ga jama’a”.

Shugaban ƙasar Seychelles, Wavel Ramkalawan, yayi imanin cewa, wajibi ne kafofin watsa labaru su faɗakar da bil’adama su gane cewa, dukkanmu iyali guda ne, kuma makomar mu na zama irin ta bai daya ne. Ƙaddamar da wannan aikin, ya nuna muhimmancin haɗin gwiwar kafofin watsa labaru na Sin da Afirka.

Ministan yawon buɗe ido na ƙasar Kenya Najib Balala ya bayyana cewa, yin magana da murya guda ƙarƙashin hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na ƙasar Sin da na Afirka zai iya yin tasiri wajen fadakar da mutane masu yawa da su rungumi ayyukan dake shafar kiyayewa da kuma gyara duniyarmu. Jawo hankalin jama’a na da matuƙar muhimmanci ga shirin kare muhalli.

A nasa ɓangaren, Yakubu Mohamed, shugaban gidan talabijin na ƙasa a Najeriya, ya ce akwai fa’ida ta musamman da kafafen yaɗa labarai ke da su wajen janyo hankalin jama’a don su maida hankali kan batutuwan da suka shafi kiyaye muhalli.

Mai fassara: Bilkisu Xin

By Editor