Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa, mutum ne mai haƙuri, ladabi da biyayya, son haɗin kai tare kuma da cikakken kishin qasa wanda ya yi faɗa da zalunci. Mutum ne shi mai kunya, marar yawan magana, mai tsantseni da kuma gudun duniya.
Tafawa Ɓalewa, Fasihi ne kuma haziƙin mutum ne wanda Allah ya ɗaukaka shi a duniya. Shi ne mutumin da duniya ta yi wa laƙabi da Mai Maƙogwaron Zinaren Afirka, wato ‘Golden Voice of Africa’ a Turance saboda zunzurutun iya maganarsa a gaban jama’a. Malamin makaranta ne shi, marubuci, manomi, sannan kuma ɗan siyasa.
Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina ƙasa domin shi ya ɗora ta a tafarkin duk wani ci gaba da muke iya gani a yanzu.
An haifi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Ɓalewa da ke Jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Nijeriya a shekarar 1912.
Ya kasance mutum mai ɗa’a da kuma asali kasancewar mahaifinsa ma’aikaci ne ga hakimin garin.
Ya yi karatu a makarantar horon malamai ta Katsina daga 1928 zuwa 1933, sannan ya zamo malami, kuma shugaban makarantar Bauchi Middle School.
Ya yi karatu a makarantar horar da malamai ta Landan daga 1945 zuwa 1946, inda ya samu shaidar malanta.
A lokacin yaqin duniya na biyu ya nuna sha’awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na Bauchi Discussion Circle.
Sannan daga bisani ya shiga siyasar malamai inda aka zaɓe shi mataimakin shugaban qungiyar malaman Arewa.
A shekarar 1952 ya zamo ministan ayyuka na Nijeriya, ministan sufuri a 1954, sannan ya zamo jagoran jam’iyyar NPC a majalisar wakilai ta ƙasa.
Ya zamo Fira Ministan farko na Nijeriya bayan da ƙasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960.
A shekarar 1966, wasu sojoji suka yi ƙoƙarin juyin mulki inda anan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe marigayi Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.
Gudunmawar da gwamnatin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ta bayar abu ne mai wahalar ƙididdigewa, kasantuwar ita ce ta kafa tubalin duk wani ci gaba da ake iya gani yau a wannan ƙasa.
• Kafa jami’o’i huɗu na Nijeriya; Jama’ar Ahmadu Bello ta Zariya; Jami’ar Obafemi Awolowo; Jami’ar Nijeriya Nsukka da kuma Makarantar Tsaro ta Ƙasa (NDA) wadda take a matsayin jami’ar sojojin Nijeriya.
• Kafa Ƙungiyar Haxin Kan Ƙasashen Afirka mai suna ‘Organization of African Unity’ (OAU).
• A shekarar 1963 gwamnatinsa ta sabunta Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
• A shekarar 1964 gwamnatinsa ta samar da dokar bayar da lambobin yabo domin girmama ’yan ƙasa da suka hidimtawa ƙasa.
Lambobin Yabo Da Girmamawa Da Aka Baiwa Tafawa Ɓalewa
• A shekarar 1952 Sarauniya Elizabeth II, ta bashi lambar yabo mai taken, OBE.

• A shekarar 1955 Sarauniya Elizabeth II, ta sa ke ba shi lambar yabo mai taken, CBE.
• Haka kuma a shekarar 1960 Sarauniya Elizabeth II, ta ba shi lambar yabo mai taken ‘Knight Commander of the Order of the British Empire’ (KBE).
• A dai shekarar 1960 aka ba shi Digirin Girmamawa daga Jami’ar Sheffield, da ke ƙasar Ingila.
A shekarar 1966, wasu sojoji suka yi ƙoƙarin juyin mulki inda a nan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe marigayi Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.
Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ya rasu ya bar mata huɗu; Jummai, Umma, Zainab da Laraba, tare da ’ya’ya 19. Daga cikin ’ya’yansa akwai Mukhtar, Sadiq, Hajiya Uwani, Umar, Ahmed, Haruna, Aminu, Hafsat, Amina, Zainab, Yalwa, Saude, Hajia Binta, Yalwa, Rabi, Ali, da kuma Hajia Talle Aishatu.
