Masu iya sayen bindiga a Zamfara da sauran garuruwa don kare kansu

Spread the love

Daga MUS’AB ISAH MARAFA

Wannan dama da Gwamnatin Zamfara ta ba wa ‘yan jiha wani cigaba ne daga inda ake yanzu. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce cikin wani Hadisin Tirmizi “wanda aka kashe wurin kare dukiyarsa ya yi shahada. Wanda aka kashe wurin kare addininsa, ya yi shahada; wanda aka kashe wurin kare jininss ya yi shahada; wanda aka kashe wurin kare iyalinsa ya yi shahada.” Musulunci bai yarda ka tsaya wani ɗan iska ya wulaqanta ka ya wulaƙanta iyalinka don kawai yana da bindiga, ko da ko kai ba ka da bindiga balle a ce kana da ita. 

Sai dai gaskiyar magana da wuya a iya kawar da matsalar tsaro ta wannan hanya? Na farko dai, ban sa ran za a ba wanda ba jami’in tsaro ba lasisin bindiga mai sarrafa kanta (bindigar da da zaran ka danne kunamar ta za ta yi ta sakin albarusai) kamar AK47 da ɓata-garin ke amfani da ita wasu lokuta. Don haka, yawanci harba-ruga ce za a ba mutane dama su saye ko kuma wata bindigar da duk bayan harbi guda sai ka sake danne-danne kafin ta sake tashi.

Na biyu kuma, manoma nawa ne ke da kuɗin sayen bindiga bayan ƴan-bindiga sun gama talauta su ta hanyar hana su noma da sace musu dabbobi da kuma amshe ajiyarsu ta hanyar fansar iyalai da ‘yan-uwansu? 

Shi fa yaƙi irin wannan dole sai an samu tsarariyar tawaga. Ni shawara ta har gobe (kamar yadda na yi ta rubutu shekarun baya shi ne, a samar da ‘yan-banga a kowacce ƙaramar hukuma da manyan gundumominsu, a yi musu horo, a haɗa su aiki da jami’an tsaro na qasa don ka da su wuce iyaka, a ba su motoci ko mashina na sintiri da bin-sawu, a ba su alawus kowane wata, sannan a ba su makamai dai-dai gwargwado. Na tuna cewa, farkon mulkin Gwamna Matawalle ya ba da umurni a ɗauki ‘yan-banga 500 (ina zaton adadin ke nan) a kowace ƙaramar hukuma, amma ba mu san in da maganar ta kwana ba. 

Don mutane biyar ko shidda ko goma ma sun riƙe bindiga a cikin ƙauye mai mutane ko da 200 ne bai hana ‘yan bindiga kan mashina hamsin kowane da goyon mutum biyu su darkake su. Ɗaiɗaikun mutane ba su iya kare kansu daga mayaƙa ba tare da gwamnati ta yi musu wani tsari da za su yi gamayya su tunkari matsalar tsaron tare ba. 

Duk da haka, wannan dama da gwamnati ta bayar tana da kyau saboda ko da ɗan-bindiga guda ko biyu ka samu harbewa kafin a kai gare ka ka rage mugun iri. kuma ka sa tsoro cikin zuciyoyin sauran ‘yanuwansa, miyagu. Saboda za su fahimci cewa su ma ana iya kai wa gare su. Sannan kuma mallakar bindiga maganin ƙananan varayi ne masu tsallaka gidajen mutane su amshe waya da kwamfuta da zinari da mota kawai don su na da wuƙa da gariyo kuma sun yi tatil da rochi. Ka mallaki bindiga, duk wanda ya tsallaka maka gida ka fyade shi. 

Musab Isa Marafa, mai sharhin ne a kan abubuwan yau da kullum

By Editor