Wa masu gidajen biredi za su yi wa yajin aiki?

Spread the love

Daga SALMAN MUKHTAR

A yau na tsinci wani labari daga kafar sadarwa ta BBC Hausa akan yajin aikin da ƙungiyar masu Gidan Biredi watau (Association of Master Bakers and Caterer Of Nigeria), ke shirin shiga a satin nan sakamakon tsadar fulawa da kayan haɗi. Al’amarin yajin aikin nasu ya gicciyar da tunanina da na wasu ire-irena a kan wa za su yi wa?

  1. Gwamnati, da ba ta da gonar noma, ba ta da alkama, ba ta da kamfanin fulawa, ba ta da gidan biredi, a ƙarshe ba ta da bakin magana ballantana ta sa baki a sassauta muku?

2.Masu noma alkama da ba wanda yake ba su kyautar taki, babu mai basu tallafin da zai sa su yi sauƙin siyar da abarsu, kai ko ka san farashin takin zamani a Naira 30,000 ma ya ɗora?

  1. Ko masu kamfanin fulawa da ba mai ba su kyautar alkama, ba mai basu tallafin kuɗaɗen da za su ƙara su sayi Alkama. Ga ba wutar lantarki da za su yi amfani da ita wajen sarrafa alkamar har ta fitar da fulawar. Na san dai ai kana da labarin nawa ake siyar da gas ɗin da suke amfani da shi a Injinan kamfanin kafin a samu fitar da garin, ko ka taɓa jin cewa kyautar Gas ake ba su ballantana su yi arahar fulawar?
  2. Ko kuma za su huce haushinsu ne a kan ma’abota cin Biredi, don su yi zuciya su riƙa siya da tsadar fiye da yadda suke saya a yanzu?
    Duk dai ta inda aka je aka dawo talaka ne a ruwa, wahalar akansa za ta ƙare. Don da yajin aiki a Nijeriya yana da rana, to da Jami’o’in Nijeriya sun shiga sahun manyan takwarorinsu da ke faɗin Duniya ta fuskar cigaba.

Salmanu Muntari, ya rubuto ne daga Kano.

By Editor