Masanan ƙasa da ƙasa sun amince da sakamakon Sin a fannin kare haƙƙin bil Adam

Spread the love

Daga CMG HAUSA

A jiya Talata ne aka kira taro mai taken “Kara ƙarfafa aikin gudanar da harkokin haƙƙin dan adama, domin kare hakkin bil adama yadda ya kamata” na hukumar kare haƙƙin dan adam ta MƊD karo na 50 ta kafar bidiyo, inda masana mahalartan taron suka yi tattaunawa mai zurfi kan batun, da yadda za a tafiyar da harkokin kare haƙƙin dan adam a faɗin duniya.

Yayin taron, malamin ilmin siyasa na jami’ar Buea ta ƙasar Kamaru Hassan Njoya, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ƙasashe masu tasowa suna fuskantar ƙalubale a fannoni guda biyu, yayin da suke ƙoƙarin kare hakkin dan adam, wato ƙasashe masu nuna fin ƙarfi suna tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran ƙasashe, haka kuma suna tilastawa ƙasashe masu tasowa, amince da manufofi irin na ƙasashen yamma, yana mai cewa, “Ya dace a girmama bambancin al’adu, da tsarin siyasa na ƙasa da ƙasa, kuma a ko da yaushe kamata ya yi a daidaita rikici ta hanyar tattaunawa, kana dole ne a yi ƙoƙari domin ingiza adalci tsakanin ƙasa da ƙasa a fannonin siyasa da tattalin arziki da sauransu.”

Malamin nazarin ilmin zamantakewar al’umma na jamilar Cork ta ƙasar Ireland Feilim Hadhmail, shi ma ya yi tsokaci da cewa, ƙasar Sin tana taka rawa ta musamman, wajen ingiza zaman lafiya, da kare haƙƙin dan adam a fadin duniya, a cewarsa: “Ƙasar Sin, babbar ƙasa ce dake taka rawa matuka a fadin duniya, a ƙasar ta Sin, al’ummomi suna da yawa, kuma tattalin arzikin ƙasar ya samu ci gaba cikin sauri, kana ƙasar tana samar da goyon baya ga ƙasashe masu tasowa yayin da suke raya tattalin arziki, kaza lika Sin ta samu amincewa daga yawancin ƙasashen duniya, a bangarorin ingiza zaman lafiya, da tattaunawa tsakanin ƙasa da ƙasa. Ana iya cewa, kasar Sin ta kasance wata gada, yayin da ake tafiyar da harkokin ƙasa da ƙasa.”

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa

By Editor