Zargin safarar sassan mutum: An tsare Ekweremadu da matarsa har zuwa Agusta

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

An tsare Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice, bayan da kotun da ke sauraron kararsu ta dage zamanta ya zuwa 4 ga Agustan 2022.

An gurfanar da ma’auratan ne a kotun Westminster Majistare kan zargin safarar sassan jikin mutum.

Wasu manyan ‘yan Nijeriya sun halarci zaman kotun, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, don nuna goyon baya ga Ekweremadu.

Tun farko, lauyan Ekweremadu, Gavin Irwin ya musanta niyyar cin zarafin yaron da lamarin ya shafa da aka ce wanda yake karewa ya yi.
Kazalika, ya ce yaron ya yi ƙarya dangane da yawan shekarunsa, sai dai mai tuhuma ya dage kan cewa lallai wanda lamarin ya shafa yaro ne.

Bisa la’akari da hukunci da Alƙalin ya yanke, ba za a ci gaba a ɗaukar wanda lamarin ya shafa, David Ukpo, a matsayin mai ƙananan shekaru ba a gaban a kotun.

Lauyan Ekweremadu ya faɗa wa kotun cewa za su miƙa takardar neman beli kafin zaman kotun na gaba da za a yi ran 4 ga Agusta.

By Editor