Tinubu ya amince ya ɗauki mataimaki Musulmi – Ganduje

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA

Gwamanna Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu ya amince zai ɗauki Musulmi a matsayin mataimakinsa.

Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan malaman jihar kusan 100 suka kai kai masa ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar.

Gidan talabijin na Channel TV ya ambato gwamnan na cewa, ”mun ba shi shawara ya ɗauki Musulmi a matsayin mataimaki kuma ya amince, saboda ba wani abu ba ne sabo a Nijeriya”.

Ya kumna yi kira ga taron malaman da su riƙa yi wa Tinubu addu’o’in samun nasara a zaɓen 2023.

Ganduje ya na ɗaya daga cikin mutanen da ake hasashen zama mataimakin Tinubu.

Sauran sun haɗa da, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai da Atiku Bagudu.

Tuni dai ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ɗauki Gwamna Okowa a matsayin wanda zai masa mataimaki a zaɓen 2023.

By Editor