Daga AMINU AMANAWA a Sokoto
Littafin ‘Daular Usmaniyya’ da ya yi tsokaci sosai kan tarihin daular mafi ƙarfi a nahiyar Afirka da na ‘Ma’a Mu’awiyah’, ya taɓo tarihi da rayuwar bajimin Malami Mu’awiyah da ma Al-fa’alul Hassan. Ma’ana, fata nagari na daga cikin littafan da matashin malami a Sakkwato Malam Nasirudden Abubakar ya ƙaddamar bayan ɗokar dogon lokaci yana rubuce-rubuce da ma duba litattafan masana.
Blueprint Manhaja ta halarci bikin qaddamar da littafan da aka ƙaddamar a makarantar haddar Alƙur’ani da sauran ilmummuka ta Sarkin Musulmi Maccixo da ke Sokoto. Ga kuma tsarabar musamman da Wakilinmu ya yi wa shafinmu na Adabi:
Matashin malamin addinin musuluncin ya ƙaddamar da littafai uku ne da suka haɗa da; ‘Al-fa’alul Hassan’, ‘Ma’a Mu’awiyah’ da kuma ‘Daular Usmaniyya’ a matsayin hanya ɗaya ta bayar da gudunmawa wajen wanzar da ilimi a cikin al’umma.
A cewar malam Nasirudden Abubakar, littafin ‘Al-fa’alul Hassan’ na son cusa ɗabi’ar kasancewa masu fatan alkhairi ga lamurran al’umma.
“Malamai suka ce, da yanzu za a ga hayaƙi ya tashi daga wani gun, to kar ka ce wuta ce, ka ce taya ce ake ƙuna, fatan alkhairi ne. Jiƙon lalle na namiji za a yi shi a tsaye, mace kuwa sai an zauna, wai fatan namiji ya je neman abinci, mace kuma ta zauna ɗakin ta daram, kaga wannan fatan alkhairi ne.”
Don haka ne a cewarsa ya yi ƙoƙari wajen rubuta littafin ne, domin al’umma su kasance masu faɗar alkhairi.
A wajen taron, Malam Abubakar Mujahid Koko ya yi bayani sosai kan littafin ‘Al-fa’alul Hassan’, watau fata nagari da Malam Nasiru ya wallafa, littafin da ya mayar da hankali kan abubuwa da dama da suka haɗa da amfani da fata tagari tun a lokacin jahiliyya da bayanin ayoyi da suka yi bayani kan kyakkyawar fata a cikin Alƙur’ani mai girma, hadissan Annabi, zamanin magabata nagari, malaman Fiƙhu da ma zamanin jihadin Daular Usmaniyya da kuma a wannan zamani na yau, inda ma ya bada misali da siyasa da kalmar kowa ya bi.
Shi ma da ya ke ta’aliƙi kan littafin ‘Daular Usmaniyya’, Farfesa Mukhtar Umar Bunza, wanda kuma shine kwamishinan ilimi mai zurfi na Jihar Kebbi, ya bayyana cewa, Daular Usmaniyya daula ce mai ƙarfin gaske a nahiyar Afrika, duk kuwa da cewa, Turawa sun so ɓata sunanta da suke kiran ta da ‘Uthmaniyya’.
“Mun sha nanata cewa, wannan daular da ba don mu mu ke da ita ba, da ‘yan’uwanmu na wani sashen ƙasar nan ke da ita, da tuni mun kasance ‘yan kallo, kasantuwar duk tsarin ilimi, shugabanci, haƙuri, cigaba, to fa daular ta Usmaniyya na da ita.
Ka ɗauki misali da sha’anin ilimin kimiyya, likitanci, shugabanci jagororin daular sun yi rubutu mai yawa akai, misalin Usulul Siyasa idan ka dube shi duk wani ilimi na “theory” ko ‘philosophy’ to akwai shi a ciki.”
A cewar Farfesa Mukhtar Umar Bunza, rubuta littafi da matashin malamin ya yi ilimi ne da bincike baya ƙarewa, don haka ne ma ya jinjina wa ƙoƙarinsa na zaƙulowa da ma aiki tuƙuru kan daular ta Usmaniyya.
Yayin da littafi na uku da malamin ya wallafa na ‘Ma’a Mu’awiyah’ (R.A) II, ma’ana “Bajimin Malami” ya samu ta’aliƙin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Sokoto, Dakta Jabir Sani Maihula, inda ya bayyana namijin ƙoƙarin Sahabi Ma’awuyyah, kasantuwar Annabi SAW da kansa yake sa shi rubuta wahayi.
Ya bayyana cewa, a cikin ‘Khudubu Sitta’ kaɗai akwai hadissan Ma’awuyyah 130, don haka duk masu biyar Ma’awuyyah alamu ne cewa suna kan hanyar shiriya.
A cewar Dakta Jabir littafin zai kasance gwarzo kasantuwar ya bada tarihin Ma’awuyyah da bayani daga ƙarni na farko har zuwa yau na manyan malamai da suka yabi Ma’awuyyah a wannan littafin mai shafuka 182.
Jim kaɗan bayan ƙaddamar da littafan uku da malamin ya wallafa, malamin ya sheda wa wakilin Blueprint Manhaja a Sokoto, Aminu Amanawa cewa, littafin ‘Al-fa’alul Hassan’ zai yi tasiri ga al’ummar Musulmi kasantuwar littafin an wallafa shi da harshen Larabci wanda shine harshen fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Malamin ya bayyana cewa, domin ƙara amfanuwar al’umma zai duba yuwar fassara littafin ‘Al-fa’alul Hassan’ da ‘Ma’a Mu’awiyah’ da Hausa ko wani yaren.
To, ko malamin ya taba wallafa wasu littattafai baya ga waɗannan? Wakilin namu ya tambaya.
“Na wallafa tsakanin muzakkira da littafai fiye da 30, amma muzakkira ta farko ita ce ‘Haƙƙatul A’ala Makkah’, amma littafin da na wallafa na farko shine ‘Ma’a Mu’awiyah’ bugu na farko, kuma Insha Allah akwai wasu 30 da na ke da burin wallafawa nan gaba, Insha Allah.”
Shi wannan littafin na ‘Ma’a Mu’awiyah’ ya samu karɓuwa ne shi ya sa aka je da yin bugu na biyu kenan?
Littafin nan ya samu karɓuwa a ciki da wajen Nijeriya, shi ya sa ma mutane suka zaburaddani cewa a buga na biyu, saboda dubin an buga shi da adadi ƙanƙani yanzu kuma an buga shi da yawa.
Kan burin da malam Nasirudden ke son cimma nan gaba, malamin cewa ya yi, “Eh akwai burika musamman dai na wallafa ƙarin wasu, kuma saƙona ga al’ummar Musulmi shine, kar su dubi ƙarancin shekaruna, ko ƙanƙantar abinda na wallafa, su dubi irin baiwar da Allah ya hore har aka yi wannan rubutu, duniya ma ana nuna shi, a duba a fa’idantu a watsa shi cikin al’umma, kuma hukuma da majalisar sarki su duba yiwuwar ɗaukar nauyin wallafa su domin yaɗuwar su a cikin al’umma.”

A yayin bikin ƙaddamar da littafin, babban baƙo a taron Ambasada Shehu Mai Wurno ya bayyana cewa, ƙaddamar da littafan da matashin ya yi wani babban ƙalubale ne ga matasa kan tashi tsaye wajen neman ilimi.
“Tabbas wannan ƙoƙarin na matashin abin a yaba ne, kuma ƙalubale ne ga matasanmu na su tashi tsaye wajen neman ilimi, domin a wannan zamanin duniya na tafiya ne da mai ilimi,” inji shi.
Malam Mukhtar Yusuf Magashi Kano a wajen taron shima ya gabatar da ƙasida mai taken “Ya Khulafa” waƙar da malamin ya yi sosai domin yabon fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun yaba matuƙa da ƙoƙarin malamin na amfani da iliminsa wajen wallafa waɗannan littafan.
Littafin ‘Al-fa’alul Hassan’ dai na da shafi 60 ne, yayin da ‘Ma’a Mu’awiyah’ ke da shafuka 180, sai ‘Daular Usmaniyya’ mai shafuka 18 kuma dukkaninsu, sun samu dubawar daktoci, farfesoshi da sauran masana a ɓangaren ilimi.
