Daga BASHIR ISAH
A ranar Alhamis, 14 ga Yulin 2022, Kwalejin Nazarin Kimiyya da Fasahar Kiwon Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta kaddamar da jarrabawar neman gurbin karatu na shekarar 2022/2023 domin bai wa masu sha’awar shiga kwalejin damar da suke buƙata.
Dalibai maza da mata daga ciki da wajen Jihar Nasarawa ne suka haɗu a harabar kwalejin da ke babbar hanyar Keffi zuwa Abuja don rubuta jarrabawar.
Jarrabawar wadda za a shafe kwana tara ana gudanar da ita, an tsara gudanar da ita ne ta hanyar amfani da kwamfuta kai tsaye, kamar yadda kodinetan shirin, Mista Emmanuel Timshana ya bayyana.

Timshana ya ce, jarrabawar ita ce irin ta farko da kwalejin ta taba shiryawa inda za a yi amfani da kwamfuta zalla wajen amsa tambayoyi a maimakon rubutu a takardar kamar yadda aka saba a baya.
Ya ƙara da cewa, jarrabawar na da sassa guda biyu, akwai ɓangaren amsa tambayoyi a kwamfuta (CBT) da kuma ɓangaren ba da amsar baka kai tsaye, wato ‘oral section’. Ya ce za a bi tsarin ƙananan hukumomi ne wajen gudar da jarrabawar.
Sa’ilin da yake yi wa Manhaja ƙarin haske game da shirin, shugaban kwalejin, Malam Suleiman A. Muhammad ya ce, domin inganta shirin jarrabawar da kuma taftace ta daga kowace irin matsala, ya sa suka sauya yanayin gudanar da ita.
Ya ƙara da cewa, duk da dai kwalejin ta jihar Nasarawa ce, amma masu sha’awar karatu a wannan makaranta daga sassan Nijeriya suna da damar shiga makarantar, don kuwa akwai wani kaso da akan ware don amfanin waɗanda ba ‘yan asalin jihar ba.

A cewar shugaban, duba da kwalejin fage ne na koyon kiwon lafiya wanda bayan kammalawa za a yi mu’amala da lafiyar al’umma, don haka ya ce ba su sakaci wajen tantance dailibai don tabbatar da waɗanda suka cancanta kaɗai aka bai wa gurbin karatu.
Daga nan Muhammad ya yi kira ga ɗaliban kwalejin da su ba da himma tare da maida hankali wajen fahimtar abin da ake koyar da su ta yadda a ƙarshe kwaliya ta biya kuɗin sabulu.
Manhaja ta gano cewa, sama da mutum dubu biyu ne suke neman gurbin karatu a kwalejin a wannan shekara.
