Larabawa sun yanke ƙauna da tsarin dimukuraɗiyyar yammacin duniya

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Wasu rahotanni da cibiyar nazari ta kasa da ƙasa ta Arab Barometer ta fitar a baya bayan nan, sun nuna cewa, galibin Larabawa sun yanke kauna da ingancin tsarin demokraɗiyyar yammacin duniya, kana an samu karin masu sha’awar tsarin ƙasar Sin.

Nazarin da aka gudanar a ƙasashe 9 da suka haɗa da Masar da Tunisia da Iraƙi da Sudan da Libya da Jordan da Lebanon da Mauritania da Palastine, sun shafi mutane 23,000.

Kuma bisa wannan nazari, cibiyar Arab Barometer ta fitar da wasu rahotanni biyu a shafinta na website a farkon wannan wata, daya mai taken “Tsarin Demokraɗiyya a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika” yayin da taken ɗayan shi ne “Ra’ayin Jama’a kan Takarar Sin da Amurka a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika”.

Rahotanni sun ruwaito cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, musamman shekaru 5 da suka wuce, mutane a ƙasashen Larabawa a Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika, na ƙara shakku game da alfanun tsarin demokradiyyar yammacin duniya, kuma ƙarin mazauna ƙasashen sun yi ammana cewa, tsarukan demokraɗiyyar yammacin duniya ba su dace da raya tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiyar al’umma ba, haka kuma ba sa ingiza gwamnati ɗaukar matakan da suka dace.

Fassarawar Fa’iza Mustapha

By Editor