NDLEA ta kama matashi da muggan ƙwayoyi a Jihar Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A ƙarshen makon da ya gabata ne Hukumar NDLEA reshen Jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wani matashi mai suna Chigozie Unama mai kimanin shekaru 28 da wasu muggan ƙwayoyin Tramadol da na Diazepam da yawansu ya kai kilogiram 34 da kilogram 32 daki-daki a cikin wasu buhuna da wasu baƙaƙen ledodi. 

A cikin wata takardar sanarwa ta musamman da ta fito daga ofishin hukumar dake Lafiya, babban birnin jihar ta Nasarawa wanda wakilinmu ya samu kwafi, an bayyana cewa hukumar ta cafke matashin ne a lokacin wani sintiri na musamman da jami’an hukumar suka gudanar akan ababen hawa ranar Lahadi da ta gabata 24 ga watan Yulin shekarar 2022 da ake ciki a babbar hanyar shiga birnin na Lafiya. 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wanda aka kaman ya yi niyyar safarar ƙwayoyin ne daga garin Onitcha zuwa Jos a jihar Filato kafin jami’an hukumar suka gano tare da cafke shi. 

Daga nan sai hukumar ta kuma bayyana cewa a halin yanzu wanda aka kama da laifin yana tsare kuma tana cigaba da gudanar da cikakken bincike a kansa kafin daga bisani ta ɗauki mataki na gaba da ya dace da laifin da ya aikata. 

A ƙarshe, sanarwar ta kuma yi amfani da damar nan inda ta gargaɗi al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya musamman matasa su guji yin mu’amala da miyagun ƙwayoyi ko yin safarar su don duk wanda ta cafke da laifin zai yaba wa aya zaƙinta. 

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ma hukumar ta NDLEA reshen jihar ta Nasarawa ta kuma yi nasarar cafke wasu da dama da laifin sha tare da safarar miyagun ƙwayoyin daban-daban a wurare daban-daban a kuma lokuta daban-daban a faɗin jihar.      

By Editor