Daga ABUBAKAR YAKUBU ABDULLAHI
“Al’adun da ku ke ƙyama, yanzu sun zama abin kwalliyar ku, saura ku karɓi addinin mu!”
Waɗannan wasu kalamai ne na izgili da wani wanda ba musulmi ba ya rubuta a ƙasan jikin wani hoton wasu ma’aurata sabbin aure, wato ango da amarya, wanda aka ɗauka lokacin wani shagalin bikin aure.
Yanayin hoton ya nuna angon cikin shigar ƙananan kaya ya sa kwat da wando da maɗaurin wuya, yayin da ita kuma amaryar ta sanya farar rigar leshi da siffar ɗinkin amaren Turawa, kai ka ce dai bukin na waɗanda ba musulmi ba ne. Ba su kaɗai ba, hatta sauran abokai da ƙawayen amarya ma duk cikin irin wannan shiga ta ƙananan kaya suka yi, wasu ma kansu babu kallabi. Sai dai mai yiwuwa ka yi mamakin jin cewa, wannan amarya da ango ’ya’yan Musulmi ne kuma ma cikakkun Hausawa ne, Amina ce da Bashir.
Ko da ya ke da gani ka san biki ne na wasu ’ya’yan masu hannu da shuni, ‘yan siyasa ko wasu hamshaƙan ‘yan boko, saboda irin yadda aka ƙawata wajen bikin da kuma irin manyan mawaƙan da aka gayyata daga kudancin ƙasar nan.
Ba ina nufin yin irin wannan shigar ta saɓawa koyarwar addini ba ne, wannan haƙƙin malamai ne su inganta ko su tsawatar a kai, amma ni abin da ya fi ɗaukar hankalina shi ne kayan da suka sa sun saɓawa bukin aure na al’adar Bahaushe. Idan mun lura, saboda saɓawar ce ma har wani ya ke ganin, saura ƙiris a ajiye addinin ma a gefe.
Na fara rubutu na da wannan salo ne domin nuna mana irin lalacewar da al’adun Malam Bahaushe suka samu kansu a ciki, musamman a ɓangaren bukin aure, kuma abin takaici masu faɗa a ji daga cikin al’ummar Arewa na daga waɗanda ke ƙara angiza irin wannan lalacewar tarbiyya da al’ada.
Abin takaici ne yau ka je wajen bukin ’ya’yan manyan ƙasar nan ka ga irin bidi’o’in da aka shirya da abubuwan da ake gudanarwa da sunan buki, waɗanda ko kusa ba su yi kama da na Hausawa ba, kuma ma ba su dace da koyarwar addini ba.
Idan mai karatu ya lura da kalaman da na rubuta a farkon wannan sharhin na san zai yi tunanin lallai sauran abokan zaman mu su kansu suna mamakin yadda garin kwaikwayon su da muke yi har mun kusa wuce makaɗi da rawa. Kalaman da aka yi amfani da su a farkon wannan rubutu ba ƙirƙira ba ne, tabbas haka wani ya rubuta a shafin Instagram na wasu masu biki da suka sa hotunan aurensu.
Ashe kenan idan har waɗanda ba Hausawa ba za su riƙa mamakin yadda rayuwar mu ta canja, muka manta da namu kyawawan al’adun muka koma kwaikwayon wasu, za mu yi takaici da cizon yatsa kan wasu abubuwan da ke faruwa a rayuwar akasarin Hausawa ko ’yan Arewa, ba kawai a sha’anin biki ba, har ma da sauran harkokin mu na rayuwa. Matasa da iyayensu sun rungumi wasu halaye da suka saɓa da asalin tarbiyya, yakana, kunya da mutunta kai da aka san Hausawa da su.
Abin da ya fi zama abin yayi a yanzu a tsakanin matasan mu shi ne, sanya kayan da suka saɓa da tsarin al’adun mu da tarbiyyar addinin mu. Idan ka ga ’yar Bahaushiya cikin sakakkun kaya masu rufe surar jiki da kamala a tare da ita to, mai yiwuwa an yi rasuwa ne ko za ta je Islamiyya ko kuma tsari da sa ido na gidan da ta fito ya takurata ta yadda tilas ta fita a haka. Amma kuwa a mafi yawan lokuta kayan da ke jikin ta matsattsu ne, masu nuna siffar jikinta, wani lokaci ma babu ko lulluɓi tare da ita. Haka su ma mazan in ba a ɗaurin aure ko wata rasuwa ta jiki ko taron mauludi da bikin Sallah ba, da wuya ka ganshi cikin doguwar riga ko babbar riga. Saboda suna ganin tsofaffin al’adu ne, na gargajiya da ba sa nuna wayewa a tare da su.
Haka idan an zo batun magana ko rubutu da harshen Hausa, za ka yi kamar ka yi kuka idan ka ji yadda ake magana da wata irin bagwariyar Hausa ko ingausa, a ɗauko Turanci a gwama da Hausa, wasu kalmomin ma sai ka rasa ma’anar su a Hausa, amma sai suna gani wai shi ne daidai, kuma wasu har da iyaye ko manyan da ya kamata sun tsawatar ko su yi gyara a maganar, amma sai dai kawai su yi dariya a kawar da kai.
Haka ma a wajen rubutun Hausa, da dama daga cikin matasan mu ba su san yadda ake rubuta akasarin kalmomin Hausa ba, sai dai su ƙirƙiro wani irin abu bisa tunanin haka ya kamata ya zama. Idan ka ga yadda ake rubuta kalmomi irin su ’yar, tsa, qya, za ka sha dariya, saboda kwata-kwata ba su ɗauki hanya ba. Ko da ya ke wani lokaci ba za ka ga laifinsu ba, saboda ba a koya musu a gida ko a makaranta ba, saboda rashin mayar da hankalin iyayen wajen koyawa yaransu muhimmancin sanin al’adun su, harshensu, da ƙa’idojin rubutunsa.
Haka ma a makarantu, ba duk makaranta ce yanzu za ka tarar akwai malamin koyar da Hausa ba, ballantana sauran harsuna. Sai an zo jarabawar kammala babbar sakandire ka ji ana cewa, yara su ɗauki darasin Hausa don su ƙara yawan sakamakon da suka samu, domin ana ganin shi ne darasi mai sauƙi. Amma ko shi ma ɗin da za a ba ka damar duba, takardun jarabawar da aka rubuta, sai ka ji kamar ka yi kuka.
A yayin wani bincike da na gudanar kan yadda ƙananan makarantu na firamare da ƙaramar sakandire ke koyawa yara ilimi da harsunan su na gado, kamar yadda dokar ilimi ta ƙasa ta ba da dama. Abin da wata Darakta a Hukumar Kula da Ilimi ta Bai Ɗaya ta sanar da ni shi ne, su kansu malaman ba su gama sanin harshen nasu ba, ballantana su koyawa wani! Don haka wannan batun ma babu shi, ana koyarwa da Turanci ne yadda za a gane kawai. Kuma hakan ne, domin kuwa in ba a ƙauyuka ba inda ake tasowa cikin al’adar amfani da harshen uwa ko harshen gado a kowacce sabga ta rayuwa, idan a birni ne ba ya yiwuwa.
Abin mamaki ne hatta a wasu gidajen watsa labarai da jaridu inda suke zama kamar makarantun koyar da harshe, za ka riƙa ji ana amfani da wata irin Hausa, ko kuma yadda ake rubuta wasu kalmomi ba a yadda suka dace ba. Saboda yadda ake ganin duk abin da ka faɗa in dai za a gane kawai daidai ne, ba lallai sai ka san ƙa’idojin amfani da su ba. Kuma wannan irin halayya ta nuna ko-in-kula da harshen gado, shi ne ya ke kai mu ga irin haka, ta yadda ingancin harshen ke qara komawa baya.
Ko da yadda wasu matasan marubuta adabi da suke ƙoƙarin nuna basirar su a harkar rubuce-rubucen Hausa, za ka tarar rubutun kawai ake zubawa ratata, babu tsari ko kiyaye sharuɗɗan rubutun littafi. Kuma yayin da ake samun wasu ƙalilan da ke neman ilimin sanin haruffan Hausa da ƙa’idojin rubutu, wasu kuwa ko oho, suna ganin in dai wasu za su gane abin da suke rubutawa to, su babu wani abu da wani zai koya musu. Shi ya sa ko kana son karanta wani labari da suka yi, sai kan ka ya kulle ka kasa karatun. Sun kasa gane cewa, duk abin da ake so a yi shi da kyau sai an koye shi, ko da kuwa cin abinci ne, yana da ladubbansa.
A rana mai kamar ta yau, akwai abubuwa da dama da ya kamata mu duba mu yi nazari a kansu su, da suka shafi rayuwar Bahaushe, al’adun sa da ɗabi’unsa. Ta yaya za a inganta su? Yaya Bahaushe a ƙarni na 21 zai dawo da kima da martabarsa, a idon sauran ƙabilu da harsuna masu tarin yawa da ake da su a ƙasar nan, Nijeriya da duniya baki ɗaya.
A yayin da wasu masana harshen Hausa da manazarta ke ƙoƙarin jan hankalin Majalisar Ɗinkin Duniya, Majalisar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika ta AU da Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, don su ba da damar amfani da Harshen Hausa a cikin manyan harsunan da za a riƙa amfani da shi wajen gabatar da jawabai, shin mu da muke tinƙaho da taƙamar mu Hausawa ne ace gudunmawa muka bayar wajen bunƙasar harshen da al’adunsa, ta yadda har wasu daga wani yanki na duniya za su gaskata cewa, lallai wannan rayayyen harshe ne mai martaba?
Idan ka shiga wasu gidajen ’yan boko na ƙasar Hausa ba kasafai za ka ji ana magana da harshen Hausa ba, ballantana ka ga an sayo littafi ko jaridar Hausa ana karantawa, don nishaɗi da ƙarin ilimi ba. Shi ya sa marubutan mu kullum a wani irin yanayi, saboda ba a damu da sayen littattafan da suke rubutawa ba, jaridun mu na Hausa kullum sai mutuwa suke yi, saboda ba a saya, musamman matasa, sai dai dattijai ko ’yan kasuwa, waɗanda su ma akasari karatun nasu bai wuce na yaƙi da jahilci ba, amma saboda kishi da son sanin halin da kasa ke ciki suke jajircewa wajen saye kowanne mako.
A rana irin ta yau, ya kamata masana da manazarta harshen Hausa su ba da himma wajen faɗakar da iyaye da sauran jama’a masu raino da haƙƙin koyarwa, su ɗauki batun koyawa yara masu tasowa yin amfani da kalmomin da suka dace na asalin Hausa da kuma koya musu rubutun ƙa’idojin Hausa yadda ya dace, don su girma da sanin muhimmancin sa a rayuwarsu, da sa musu kishin harshen don su zama masu alfahari da shi a ko’ina. A maimakon karaɗe zaurukan sada zumunta kamar yadda aka saba kowacce shekara, ana gasar rubuta kalmomin Hausa ko karin magana. A riƙa shirya taruka tsakanin ƙungiyoyi, ana tara malamai, manazarta da ’yan jaridu, domin tattauna batutuwa da ƙalubalen da suka shafi rayuwar Hausawa da harshen Hausa, da kuma yadda harshen ko al’ummar sa za su kawo wa duniya canji da cigaba. Shirya raye-rayen gargajiya, bayyana sutura da girke-girken al’adun gargajiya na Hausawa da baje kolin rubuce-rubucen tarihi da nishaɗantarwa da masana ilimin harshe suke samar wa.
Bincike ya nuna cewa, Ranar Hausa ko kuma Hausa Day da Turanci, rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen ya ke fuskanta, wanda aka fara raya bikin a shafukan sada zumunta musamman ta shafin Twitter da niyyar haɗa kan masu magana da harshen Hausa. An zavi ranar 26 ga watan Augusta ne domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan “q” da “x” da “v” wanda babu su a haruffan Turanci.
A ganina ya kamata mu kalli fiye da wannan, a riqa zurfafa bincike wajen fitar da ta ke ko darasi da za a mayar da hankali a kansa wajen bikin wannan rana, don ya dace da yanayi ko lokacin da ake ciki, da nufin duba irin gudunmawar da Bahaushe ke bayarwa a wannan ɓangaren.
A yayin da nake yabawa da gudunmawar da waɗanda suka jajirce wajen raya bukin wannan rana irin su Malam Abdulbaƙi Jari, ma’aikacin BBC Hausa, wanda aka ce shi ya fara bai wa wannan rana muhimmanci a harkokin da ya ke yi a zaurukan sada zumunta, manyan masana harshen Hausa, irinsu Farfesa Ibrahim Malumfashi, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da sauran fitattun manazarta bisa gudunmawar da suke bayarwa a kowanne lokaci don ganin harshen Hausa ya samu haɓaka da samun karvuwa a duniya. Domin ayyukansu ne suka sa har aka kawo wannan lokaci, inda a yau Jumma’a, 26 ga watan Agusta ake gudanar Ranar Hausa ta Duniya a karo na 8, a matsayin harshe na goma sha ɗaya mafi tasiri a duniya, da aka fi amfani da shi.
Taken bikin ranar na bana, Muhimmancin Zaman Lafiya Ga Al’umma, na so ne ya duba gudunmawar Hausawa ga cigaban zaman lafiya da tsaro a yankunan ƙasar Hausa, duba da irin ƙalubalen da yankin ke fuskanta na taɓarɓarewar tsaro da rashin zaman lafiya tsakanin Hausawa da maƙwaftansu.
Allah ya maimaita mana na baɗin baɗaɗa cikin masu rai da lafiya!
