Jarrabawa ba a nuna ƙwarewar malamin firamare: Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna

Spread the love

Daga SULAIMAN S. MAI BAZAZZAGIYA (Phd)

Ya mai girma Gwamna, na san kai ba za ka san ni ba. A yanzu ina ɗaya daga cikin ma’aikatanka. Sannan kuma na yi aiki a ƙarƙashinka a lokacin kana Minista a Abuja.

Alal haƙiƙa, ka yi abubuwa da dama na farfaɗo da ilimi a Birnin Tarayyar Abuja. A lokacin wanda ka ɗora wa alhakin wannan aiki shi ne Sakataren zartaswa, Dakta Awwal Anwar, Malami daga Jami’ar Bayero Kano. Ya tafiyar da abubuwa bisa tsari.

Kowa ya yaba aikin da kuka yi. Misali, kun fito da tsarin alawus ɗin birni zuwa ƙauye. A wannan tsari, malaman dake koyarwa a ƙauyaku sun fi morewa. An raba mana kwamfutoci a cikin sauƙi da babura. A lokacin ma’aikatan Ofis da yawa sun bar Ofis sun dawo koyarwa saboda kyakkyawan tsari da kyautatawa da kuka yi wa malamai.

A lokacin malamai an tura su karo ilimi. Ina cikin wanda aka tura Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya (ABU), domin yin karatun digiri na biyu. Haka nan an tura mu mun yi PGDE.

Mai girma gwamna, a nan jihar Kaduna sai na ga abubuwa akasin haka. Ban san inda matsalar take ba. Hausawa na cewa: “Ba a mugun Sarki sai mugun bafade.” Ƙila mashawartanka ne suke yi maka ‘Iza mai kantu ruwa’. Ana yi maka zagon ƙasa.

A ce a duk faɗin Nijeriya, jihar Kaduna ce kawai shekara ta bakwai mun shiga ta takwas, amma ba a gama tantance malamai ba? Bayan ga makarantu sun cika sun tumbatsa babu isassun malamai. A cikin aji ana samun ɗalibai fiye da ɗari biyu. Tun lokacin da aka sallami malamai 25,000 har yanzu al’amura ba su inganta ba.
Misali, na saurari wani daga jami’an da ke tantance malaman Firamare a jihar Kaduna yana bayani a wata kafar sadarwa cewa: “Za a sake bai wa wasu malamai dama ta ƙarshe su sake jarabarawar da aka yi masu. A ƙa’idar jarabawar, ana so malami ya ci 100% Saboda jarabawar da ake yi wa malaman ta ‘yan aji huɗu na Firamare ce. Amma an sassauta zuwa kaso 75%. Saboda haka, a yanzu duk wanda ya samyi maki 40-74% su ne aka ba su dama ta ƙarshe su sake rubuta jarabawar.

Ya mai girma Gwamna, a binciken da na gudanar, waɗannan su ne darussan da aka gwada dukkan malaman a yankin Zariya ban san wasu sassan ba:

  1. Harshen Turanci
  2. Lissafi
  3. Kimiyya.
  4. Soshiyal sutodi
  5. Pedagogy

Waɗannan su ne darussan da ake so duk wani mai son ci gaba da aikin koyarwa a makarantun Firamare a jihar Kaduna sai ya samu 75%.

A cikin malaman nan akwai malaman koyar da darasi. Kamar masu koyar da harshen Hausa da Arabiyya da Faransanci Sannan akwai malaman addinin Musulunci da na Kiristanci. A cikin su akwai masu shekara 30 abin da suke koyarwa ke nan. Ba su taɓa koyar da waɗancan darussa ba. Da rana tsaka, sai a kira su zuwa jarabawa a kan waɗancan darussa a ce duk wanda bai ci su ba, an kore shi.

Ke nan duk malamin harshen Hausa ko na Arabiyya ko na addini, idan bai ci darasin lissafi, da ilimin kimiyya ba zai iya koyar da su ba.

Na san wani zai ce ai lokacin da suke karatun NCE, ko B.A.Ed. ai sun karance su. To amma ga masu NCE waɗanda su ne suka fi yawa, ana cewa ne su ƙware a darussa biyu misali, Hausa-Arabiyya.

Saboda Allah ina adalci a ce fannin da ka karanta ba a gwada ka a kansa ba, kawai sai a kore ka. Wani ban haushi, dukkan jarabawar nan Yes ko No ce, kuma da Kwamfuta. Sannan kowace kwamfuta an ba ta lokaci, lokaci na yi za ka tsaya. Wani lokaci kuna cikin jarabawar yanar gizo zai tsinke.

Sannan a duba malamai da ke cikin karkara, waɗanda ba su iya sarrafa kwamfuta ba. Ire-iren ƙauyukanmu kamar: Kwatakware, Ɗan damisa, Likoro, Taba, Kudan, Tashar Dauda, Katanga, Shika. A wani ƙauyen ma ba wutar lantarki. An tura malamai suna hakuri da mutanen ƙauye. Yanzu an ɗauki wasu waɗanda ba su da sha’awar koyarwar. Kullum neman canjin wajen aiki suke yi.

Shawarata ga mai girma Gwamna

Idan dole sai an yi jarabawa, to kowane malami a gwada shi a fanninsa. A sa shi ya shiga aji ya koyar a gani idan ya gaza, a ba shi horo na musamman ko a canza masa wurin aiki.

Idan ana son duk malami ya sami ilimin kwamfuta, sai a tallafa masu su saya. A ba su horo na musamman, kamar yadda kuka yi mana a Abuja.

Ya mai girma Gwamna, yawan tankaɗe da rairayar da ake yi wa malamai, yana sawa hatta waɗanda suka ci jarabawar, ba su cikin kwanciyar hankali. Idan mutum kullum na fargaba, ba zai sami natsuwar koyarwa ba.

Muna fatar za a duba waɗannan shawarwari. Ina da tabbaci kana da kyakkyawar ƙuduri na ganin ci gaban ilimi a jihar Kaduna, to amma a fahimtata akwai inda aka sami matsala. A kafa kwamitin ƙwararru a zavo malamai daga Jami’o’i da Kwalejojin ilimi na Jihar Kaduna su ba da shawara. Kada a dogara da ma’aikatar ilimi ta Jihar Kaduna, a haɗa su da wasu daga waje.


Ra’ayina game da jarrabawar da Malam Nasiru El-Rufai yake wa malaman firamare a Kaduna

An sanya malaman Firamare rubuta jarabawa da na’urar kwamfuta, wasu ba su da ilimin kwamfuta sun faɗi, an kore su. Wannan ba shi ke nuna ba su da ƙwarewa a fannin da suke koyarwa ba ya mai girma Gwamna Nasiru El-Rufa’i.

Akwai tsofaffin malamai masu tarbiyya kuma su tarbiyyantar da yara, domin sun faɗi wannan jarabawa sai a kore su a ɗauko masu ilimin kwamfuta ko da ba su da tarbiyya. A duba wannan batu.

Me zai hana a ba su lokaci domin su je su koyi ilimin kwamfuta kafin a yi masu jarabawar da ita? Na san ka yi makamancin haka lokacin kana Minista a Abuja.

Ina iya tunawa a lokacin ina koyarwa a Abuja ka fitar da doka cewa kowa ya nemi ilimin kwamfuta. Sannan ka ba mu tallafi wajen sayen Kwamfuta ta hannun wani kamfani. Tawa har yanzu tana nan tun 2007.

Abin mamaki game da wannan jarabawa, wasu ba su yi jarabawar ba, amma an ba su makin jarabawar. Akwai wadda aka ce ta yi shekara biyu da ritaya, amma sai ga shi ta ci jarabawar. Wasu kuma komputar babu NETWORK ba su yi komi har lokaci ya cika. Duk an haɗa an kore su, da waɗanda ba su rubuta jarabawar ba.

A riqa sara ana duban bakin gatari. Rashin aiki na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara haɓakar da rashin tsaro a ƙasa. Idan aka kori iyayen yara aiki, idan iyaye sun kasa ɗaukar nauyin ‘ya’yansu a makaranta, ƙarshe su koma ta’addanci.

Mai tarko ba ya ɗaga kara, kai dan siyasa ne, ga zaɓe ya kusanta, kun tsayar da ‘yan takara a jam’iyyarku ta APC, tun daga kan shugaban ƙasa, a yo ƙasa zuwa ga ɗan majalisar jiha.
Domin Allah a ɗaukacin malaman nan da kuke kora, da iyalansu da dangoginsu da masoyansu, waye zai yi maku fatan alheri a cikin su na cin zaɓe? Musamman wannan lokaci da duniya ta ɗauki zafi yunwa na cusa wasu kaburbura, musamman talakawa. A dai-dai wannan lokaci a ce ana korar ma’aikata. Ba wata jiha a yanzu da za a ce ana korar ma’aikata. Ƙuri’a ƙwara ɗaya na da muhimmanci ga ɗan siyasa.

Kada ka shafa wa ‘yan takararku kashin kaji. A yanzu da aka kaɗa kugen siyasa, masu zabe ana lallashin su ne, kamar talaka ya je neman auren Gimbiya ‘yar Sarki.

Don Allah a tausaya wa waɗannan malamai da aka kora fiye da 2000. Korar fa waɗannan, idan ka haɗa da ‘ya’yansu da dangoginsu, da suka dogara a wuyansu, wajen mutum dubu 20,000 ka saka cikin ƙuncin rayuwa. Ba wai su kaɗai ma’aikatan abin zai shafa ba. Allah mai tausayi ne kuma yana son masu tausayi.

Alhamdulillahi. Mai girma Aminu Abdullahi Shagali, yakamata a ba gwamna shawara. Wannan aikin ofishinka ne.

Allah ya sa Gwamna ya amsa wannan roƙo.

Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya malamin jami’a ne mai sharhin a kan al’amurra. Ya rubuto ne daga Kaduna.

By Editor