Da yiwuwar Ronaldo ya koma Napoli da buga wasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Duk da rashin tabbas ɗin da ya mamaye ƙoƙarin Cristiano Ronaldo na sauya sheƙa zuwa ƙungiyar da ke cikin gasar Zakarun Turai, a halin yanzu alamu na nuni da cewar ɗan wasan zai iya raba gari da ƙungiyarsa ta Manchester United.

Bayanai daga sahihan majiyoyi cikinsu kuwa har da jaridar Corriere della Sera da ake wallafawa a birnin Milan, sun nuna cewar akwai yiwuwar Ronaldo mai shekaru 37 zai koma taka leda ne a Napoli, a kakar wasa ta bana.

A baya-bayan nan wakilin Ronaldo, Jorge Mendes, ya sanar da ƙungiyar na Seria A, cewa United za ta biya Yuro miliyan 100 don sayen ɗan wasanta na gaba Victor Osimhen, cinikin da zai bai wa Ronaldo damar yin sauyin sheƙar da ya ke fata cikin sauƙi.

A halin da ake ciki, Napoli ta sanya farashin Yuro miliyan 130 ne ga duk wanda ke son ƙulla yarjejeniya da Osimhen, sai dai ana kyautata zaton ƙungiyar za ta iya rage yawan kuɗin idan har za ta samu damar ɗaukar Cristiano Ronaldo.

A wani labarin kuma, Casemiro ya yi fatan Ronaldo ya ci gaba da zama a Manchester United

Sabon ɗan wasan tsakiyar da Manchester United ta sayo daga Real Madrid, Casemiro ya yi fatan Cristiano Ronado ya ci daf a da zama a Old Trafford, duk kuwa da cewa ana ta danganta ɗan ƙasar Portugal ɗin da sauya sheƙa.

Casemiro wanda ya taɓa wasa da Ronaldo a Real Madrid, ya koma Manchester United ne a makon jiya kan farashin da ya kai fam miliyan 70, wanda ke nuna zai zama ɗan wasa na 3 mafi ɗaukar albashi a ƙungiyar mai doka gasar Firimiyar Ingila.

Casemiro wanda ya ce Ronaldo ya riga ya fara taimaka masa wajen fahimtar sabon muhallinsa, ya bayyana shi a matsayin ɗan wasan da babu irinsa a duniya yanzu.

Ronaldo ya yi zaman ɗumama benci a wasan da Manchester United ta doke Liverpool da ƙwallaye 2-1 a ranar Litinin ɗin da ta gabata, abin da ya zafafa raɗe-raɗin cewa zai bar ƙungiyar zuwa wadda za ta doka gasar zakarun nahiyar Turai.

Sauya sheƙar Casemiro ɗan ƙasar Brazil zuwa Old Trafford ya bai wa da dama mamaki, ganin cewa ya bar ƙungiyard a ta lashe gasar zakarun Turai zuwa wadda ta gama a matsayi na 6 a gasar firimiyar Ingila, amma ɗan wasan ya ce a shirye ya ke ya fuskanci sabon ƙalubale.