Man United za ta ɗauki Antony kan sama da fam miliyan 80 daga Ajax

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Manchester United ta amince za ta ɗauki ɗan ƙwallon Ajax ɗan ƙasar Brazil, Antony.

Ana cewar United za ta sayi ɗan wasan kan sama da fam miliyan 80.75 da ƙarin tsarabe-tsaraben fam miliyan 4.25.

Nan gaba kaɗan ɗan wasan mai shekara 22 zai je Manchester, domin a auna ƙoshin lafiyarsa, daga nan ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniya.

Antony zai yi kafaɗa-da-kafaɗa da Harry Maguire a matakin waɗanda ta ɗauka da ɗan karen tsada – Paul Pogba ne mafi tsada da United ta saya daga Juventus kan fam miliyan 89 a tarihin ƙungiyar.

Antony ne na huɗu mafi tsada da aka saya a Firimiyar Ingila:

Mai buga tamaula daga gaba zai zama na biyar da United ta ɗauka a bana, bayan Lisandro Martinez da Casemiro da Tyrell Malacia da kuma Christian Eriksen wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford.

Antony ya taka rawar gani a Ajax da cin ƙwallo 47 a dukkan fafatawar da ya yi mata kaka biyu.

Ɗan wasan ya nuna kwarewarsa ƙarƙashin Erik ten Hag a Ajax, shi ne kocin ya ɗauke shi zuwa Manchester United.

Antony, mai shekara 22 zai zama na huɗu da aka saya a Premier League da tsada, bayan Paul Pogba da ya koma Manchester United, sai Chelsea da ta kara ɗaukar Romelu Lukaku da kuma Jack Grealish da Manchester City’ ta ɗauka.