Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamna Gandujen na Jihar Kano

Daga AMINU ƊAN ALMAJIRI

Zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Da Fatan kana nan cikin ƙoshin Lafiya.

Dalilin Rubuta Maka Wannan saƙo shi ne, a yau na ci karo da wani labari na wani gini da kake mai suna ‘Kano Emirate Mega Secondary School’.

Haƙiƙa kam ginin ya yi kyau, ga shi na ga an ce sauran gundumomin Kano duk ana irin wannan gini, Allah Ya taimaka. Sai dai hanzari ba gudu ba ya Malam Gwamna…

A Kano muna da makarantu daban-daban da suka lalace, wasu gyaran nasu kaɗan ne, wasu kuwa ginin ne yake da buƙatar sabuntawa. Makarantun nan da ake maganar su, za a iya samun kowane aji yana ɗaukar ɗalibai da ba za su gaza mutum 70 ba. Idan kuwa har aka ce ajin da wannan yaran suke zaune ya lalace, menene makomar karatunsu? Menene makomar gobensu idan suka saba da zama babu zuwa makaranta?

Malam gwamna, na san aƙalla kowane gini da kake yi na sakandaren nan a kowace gunduma ta jihar kano, ginin zai iya cin kuɗin da ba za su yi ƙasa da miliyan 50 ba.

Malam Gwamna idan da kowace makaranta da take da matsalar gini ko rufin ajujuwanta za a kashe mata miliyan 1, da kuwa an yi maganin rashin zuwan ɗalibai makaranta, sannan ƙudurinku na ilimi dole zai tabbata a jihar kano.

Idan kuwa aka bar ajujuwan makaranta musamman na Firamare a lalace, sannan aka je aka kirkiri sabon gini domin ‘yan sakandare, ina ganin zai iya zama cewa ana tufka ne ta baya tana warwarewa.

Babban abin ma tsoro da tashin hankalin shi ne, musamman yanzu muna lokaci na damuna, wasu ajujuwa duk da lalacewar su ana iya zama idan ba lokacin damuna ba ne, idan kuwa lokacin damina ne, to waɗannan ajujuwan kamar an basu hutu ne. Saboda babu ajin da za a kai su a zaunar da su, duba da matsugunin ɗaliban ya yi kaɗan.

A nan nake qara amfani da wannan dama wajen kira ga ma’aikatar Ilimi. Ya kamata ku inganta sha’anin banɗakuna mata a makarantun sakandare, saboda yanayin da ake ciki a wasu makarantun na mata babu daɗin ji, balle gani. Ku sanya idanu matuƙa, idan laifin na hukumar makaranta ne, a tsawatar, idan naku ne, to ku gyara.

Amma harkar sha’anin banɗaki na mata, musamman a makarantar ‘yan mata ta masaqa dake gwammaja, babu daɗi sam. Domin duk mai hankali idan ya je ya ga yanda banɗakuna suke, abinda zai fara tambayar kansa, yaya ɗaliban suke idan buƙatar shiga banɗaki ta kama su?

Duk da dama sha’anin harkar Ilimi a Kano ya hango ramin kabarinsa, saboda riƙon sakainar kashi da sakaci da aka yi a kansa, amma duk da haka, a fara gyara waɗanda ake da su kafin a samar da waɗanda babu su a zahiri.

Allah ya ɗaukaka jihar Kano, Ya wanzar da zaman Lafiya a Kano da Nijeryia bakiɗaya.

Aminu Ɗan Almajiri, ya rubuto daga jihar Kano.