Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa ta rufe makarantu 46 a Jihar Bauchi

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa ta rufe makarantun koyarwa da cibiyoyin karatu masu samar da takardun shaidar karatu na NCE guda 46 dake koyarwa a faɗin Jihar Bauchi.

Wannan rufewa ya biyo bayan wata wasiƙa ta ranar Laraba, 5 ga watan Satumba da hukumar ta aika wa kwamishinan Ilimi na jihar, Dokta Aliyu Usman Tilde, tana mai cewar, dukkan makarantun da rufewar ta shafa an basu wa’adin kwanaki talatin ne na bin umarni ko su fuskanci fushin doka.

Wasiƙar, wacce babban sakataren hukumar Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle ya sanya hannu, ta yi tuni da cewar, hukumar a watannin Oktoba da Nuwamba na shekara 2021 ne ta yi rangadin tantance makarantun, domin ta zaƙulo waɗanda suke koyarwa da samar da takardun shaida na NCE ba bisa ƙa’ida ba, rangadin da hukumar ta gudanar tare da haɗin kan ma’aikatar ilimi na jihar.

Farfesa Paulinus Okwelle ya ce rahoton wancan rangadi da hukumar su ta gabatar wa ma’aikatar ilimi ta tarayya, shi ne ya haifar da wannan umarni na rufe makarantun na jihar Bauchi da yanzu aka haramta wa koyarwa.

“Hukumar saboda haka take jawo hankalin gwamnatin Jihar Bauchi bisa wannan umarni, tare da neman haɗin kanta domin ta tabbatar an rufe waɗannan makarantu na jihar.”

Wasiƙar ta fayyace wa kwamishinan ilimi na Jihar Bauchi dukkan makarantun guda 46 da suke barbaje a faɗin jiha da aka yi umarnin rufe su cikin gaggawa.

Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle ya ce, “dangane da wannan lamari, kwalejohi da cibiyoyin koyarwa da wannan umarni ya shafa an ba su wa’adin kwanaki talatin na rufe makarantu, ko kuma su ci karo da doka.”

Idan za a tunawa dai, majalisar dokoki ta jihar Bauchi a watan Yuli ne na shekarar da ta gabata, 2021 ta nuna fushinta bisa haramtattun makarantu barkatai dake sassa daban-daban na jiha suna koyarwa haɗi da samar wa yara takardun shaida ta NCE ba tare da bin ƙa’idoji ba.

By Editor