2023: Rundunar ’Yan Sanda ta ja kunnen dogarin matar Atiku bisa riƙe mata jaka

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ja kunnen wata ’yar sanda da har yanzu ba a bayyana sunanta ba, saboda riƙe jakar Titi, matar ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a Babban Zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ’yar sandar da ta kasance dogari ga matar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar.

Matar Atiku Titi, a ranar Laraba, 5 ga Oktoba, 2022, ta gabatar da wani shiri da ya mayar da hankali kan mata a Abuja kuma mijin nata ya raba hotuna daga taron, wanda ya nuna ta a tsaye da ’yar sanda tana riƙe da jaka a bayanta.

Kafofin sada zumunta sun cika da cece-kuce tun lokacin da aka yaɗa hotunan, inda jama’a suka kira lamarin da rashin mutunta kai da ’yan sandan Nijeriya ke yi.

Da ya ke mayar da martani kan hotunan, Kakakin Rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ta shafinsa na Tuwita, ya yi Allah-wadai da matakin da jami’an tsaro su kan ɗauka, inda ya ƙara da cewa, za a yi mata kamun kifi domin a sanya mata takunkumin da ya dace.

Adejobi ya bayyana abin a matsayin “mummuna” ga masu bin doka da oda don ɗaukar jakar matayen shugabanni, yana mai cewa irin wannan matakin yana sa su gaza yin aikin ‘yan sanda.

Ya ƙara da cewa, ba za a bari a ci gaba da gudanar da irin wannan aiki a cikin tsarin ba kamar yadda ’yan sanda ke da niyya wajen gyara tsarin aiki.

By Editor