Ambaliyar Lokoja ta zama barazana ga Abuja

*Gwamnati ta ɗora alhakin ƙarancin mai a Babban Birnin Tarayya kan ambaliyar
*Ta gargaɗi matafiya masu bin hanyar Abuja zuwa Lokoja

Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M. MUHAMMAD

Wata gagarumar ambaliyar ruwa da aka yi kuma ake hasashen cigaba da yi a ’yan kwanakin nan a garin Lokoja da ke kan hanyar zuwa Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, daga yankin kudancin ƙasar, ta yi sanadiyyar haifar da gagarumar barazana ga mazauna Babban Birnin Ƙasar ta fuskar walwalar rayuwarsu, domin ba ɓarkar kawai da ambaliyar ta yi a Lokoja ce kaɗai ta shafi al’ummar ƙasar ba, har ma da matafiya da kuma mazauna Abuja.

Garin Lokoja, ko Lokwaja, kamar yadda wasu ke kiran sa, yana da nisan kilomita 163 daga Abuja. Shin ta yaya wannan ambaliya ta zama barazana ga mazauna Babban Birnin Tarayyar? Ga irin rahotannin da Wakilan Blueprint Manhaja suka tattaro ma na:

Yadda ambaliyar ta zama silar ƙarancin mai a Abuja – Gwamnati

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya ‘Midstream and Downstream Regulatory Authority’ (NMDPRA), ta ce, ambaliyar ruwa da aka yi a Lokoja ne ya haddasa komaɗar layukan gidajen mai a babban birnin tarayya da kewaye.

A cikin wata sanarwa da sashen sadarwa na hukumar ya sanya wa hannu, ta ce, ambaliyar ruwan ta mamaye wani kaso mai yawa na hanyar zirga-zirgar ababen hawa ke da zuwa Abuja.

“Hukumar na son bayyana layukan man fetur ne sakamakon ambaliya da ba a tava ganin irinta ba a Lokoja, jihar Kogi, wanda ya mamaye babban birnin jihar tare da daƙile duk wani motsi na motoci.

“Wannan abin baƙin ciki ya shafi rabon albarkatun man fetur ga babban birnin tarayya Abuja da kewaye,” inji sanarwar.

A cewar NMDPRA, tana bayar da shawarar ne domin baiwa ’yan Nijeriya damar fahimtar dalilin yin layukan da ake yi a gidajen mai.

Hukumar ta ba da tabbacin cewa “A matsayin wani ɓangare na matakan shawo kan lamarin, ana ci gaba da safarar man fetur a manyan motoci ta wasu hanyoyi. Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa akwai isassun albarkatun mai a cikin ƙasa.

“Saboda haka, ana shawartar jama’a da su guji shiga firgici a gidajen mai saboda hukumar NMDPRA tana aiki tuquru tare da masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati don tabbatar da samar da man fetur a faɗin ƙasar nan. Hakazalika, an shawarci ’yan kasuwa da su daina tara mai don kada su jawo wa ’yan Nijeriya wahala.”

Hukumar ta ce, ta himmatu wajen ganin an samar da wadataccen man fetur da kuma rarraba albarkatun man fetur a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi matafiya:

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi matafiya musamman masu ababen hawan da ke bin hanyar Abuja zuwa Lokoja, saboda mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye daidai Koton-Ƙarfe.

Babban Jami’i mai Kula da Ayyuka na Gwamnatin Tarayya a Kogi, Injiniya Jimoh Kajogbola shi ne ya yi wannan gargaɗi a cikin jawabinsa ga manema labarai a Lokoja, ya shawarci matafiya da su nemi wata hanyar domin tsira da rayukansu.

Ya ce, “sakamakon ambaliyar ruwan da ake samu a ƙasar, Kogin Neja ya cika ya tumbatsa har ya yi ambaliya akan tagwayen titin Koton-Ƙarfe wanda kuma babbar barazana ce ga masu bin hanyar.

“Masu zuwa Abuja daga Kudu maso Yamma ana shawartar su da su bi ta hanyar Ilorin zuwa Mokwa su ɓulla ta Bida, haka kuma matafiya daga Gabashin ƙasar da Kudu maso Kudu su kuma ana shawartar su da su bi ta hanyar Makurdi zuwa Lafiya.”

Ya roƙi mutane da ko dai su yi amfani da hanyar Abuja zuwa Lafiya zuwa Makurdi zuwa Otukpa ko kuma hanyar Abuja zuwa Bida zuwa Mokwa har Jebba, zuwa nan da lokacin da ruwan Koton-Ƙarfe zai janye.

Kamar yadda rahotanni dai suka nuna, ambaliyar ta mamaye zuwa bakin sabuwar gadar da ake ginawa a garin Koton-Ƙarfe wanda ya hana motoci bin hanyar a ranar Litinin.

Hakan ya haifar da cinkoson motoci manya da ƙanana da ke ƙoƙarin su wuce amma abin ya faskara.

Lamarin ya qara dagulewa ne a lokacin da wasu manyan motoci suka maƙale a ‘yar hanyar da ake ratsawa a wuce, wanda hakan ya jefa motoci da yawa da sauran matafiya cikin tsaka-mai-wuya sakamakon rashin matsawa ko’ina daga inda suke.

Jihar Kogi na ɗaya daga cikin jihohin da ambaliyar ruwa ta fi shafa, sakamakon kasancewar kogin Binuwai da Neja da suka haɗu a Lokoja, suka kuma cika da ruwa suka tumbatsa a wannan shekarar.