Nijeriya a 62: Har yanzu akwai jan-aiki a gaba

Yayin da Nijeriya ke cika shekara 62 da samun ’yancin kai, abin takaici har yanzu ƙasar na fama da matsaloli da ɗimbin alƙawuran da ba a cika ba. Matsalar rashawa da cin hanci ne dai babban ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, al’amarin da ya haifar da kusan dukkannin matsalolin da ‘yan ƙasar ke fama da su. Lokaci ya yi da za a sake yin nazari a kan hanyar da za a bi wajen samun ingantacciyar ƙasa ta dimokuraɗiyya da kuma tsara mafi kyawun hanyar cigaba.

Wannan tafiya ta kasance mai wahala tun daga farko. Misali shekaru shida bayan samun ’yancin kai, an yi juyin mulkin da ya kai ga kifar da gwamnatin farar hula ta lokacin. Rikicin da ya ɓarke bayan wancan juyin mulkin ya kai ga yaƙin basasa a shekara ta 1967. Yaƙin ya kawo ƙarshe a shekarar 1970, amma tun daga lokacin ake samun rashin jituwa da gaba da juna a tsakanin ƙabilu daban-daban na ƙasar.

A shekarar 1979, an samu sauyi daga mulkin soja zuwa gwamnatin farar hula, wanda ya kai ga bikin rantsar da shugaban ƙasa Shehu Shagari. A shekarar 1983 ne aka sake zaɓarsa a karo na biyu a kan karagar mulki amma ba da daɗewa ba ’yan mulkin kama-karya na soji suka hamɓarar da shi. Daga baya sojoji masu fafutuka ne suka yi mulkin Nijeriya daga 1983 zuwa 1999 lokacin da aka samar da jamhuriya ta huɗu.

Tun daga shekarar 1999, ba a samu tsaiko daga sojoji a harkokin mulkin ƙasar ba. Daga Cif Olusegun Obasanjo, wanda ya mulki tsakanin 1999 zuwa 2007, zuwa Marigayi Shugaba Umaru ’Yar’adua, wanda ya mulki daga 2007 zuwa 2010 da kuma Dr. Goodluck Jonathan, wanda ya karvi mulki bayan rasuwar ‘Yar’aduwa, yanzu kuma ga shugaban ƙasa mai ci Muhammadu Buhari. A mulkin Buhari, Nijeriya ta ci gaba da tafiya duk da rashin jituwa a tsakanin ’yan ƙasar da ke naman wargaza ta.

Wannan, duk da haka, yana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya. Misali, matsalar rashin tsaro na ƙara ta’azzara a kowace rana. Tun bayan sace ’yan matan makarantar Chibok da aka yi a shekarar 2014 a jihar Borno, wannan ta’addancin ya kunno kai ta yadda dubban ’yan makaranta sun tsinci kansu a yanayin.

A cikin al’umma masu yawa, lamarin bai bambanta ba. Sau da yawa ‘yan ta’adda suna yin garkuwa da matafiya. Babu inda ya ke lami-lafiya. An kai hare-hare a gidajen yari, titin jirgin ƙasa har ma da filin jirgin sama. Muna da tarihin da ba za a iya mantawa da shi ba a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe masu fama da matsalar ta’addanci a duniya.

Halin tattalin arziki wani babban tsaiko ne a yunƙurin ƙasar na samun cigaba. A yau, kusan dukkanin alamun cigaban tattalin arziki babu su. Talauci ya yi ƙamari yayin da sama da kashi 80 cikin 100 na ‘yan Nijeriya ke rayuwa cikin talauci. Adadin rashin aikin yi ya haura kashi 33 cikin ɗari. Yawan hauhawar farashin kayayyaki ya yi ƙamari cikin shekaru 17 da ya kai kashi 20.5 cikin 100.

Adadin bashin da ake bin ƙasar ya haura zuwa Naira Tiriliyan 42.85 daga Naira Tiriliyan 21.725 da ya kasance a shekarar 2017. An yi hasashen zai kai sama da Naira Tiriliyan 60 nan da shekarar 2023. A shekarar 2020, ƙasar ta fuskanci koma bayan tattalin arziki mafi muni tun a shekarun 1980 kuma na biyu cikin shekaru biyar. Babban abin takaici shi ne cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke haƙo ɗanyen mai a duniya.

Ilimi, wanda shi ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma, yana neman rugujewa. A wani rahoto na baya-bayan nan, Hukumar Kula da Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ƙiyasta cewa, adadin yaran Nijeriya da ba sa zuwa makaranta ya haura daga kimanin miliyan 12 a shekarar 2021 zuwa kusan miliyan 20 a yanzu.

Mafi muni shi ne yadda ɗaliban jami’o’in gwamnati ke fuskantar tsaikon karatu a sakamakon tsawaita yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’in (ASUU) ta shiga. Yajin aikin na ɗaya daga cikin jerin yajin aikin da ƙungiyar ta fara tun a shekarar 2009 lokacin da ta qulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya kan hanyoyin farfaɗo da ilimin jami’o’in ƙasar nan.

A lokacin da ake yin juyin mulki, abin da sojojinmu suka yi a duk lokacin da suka karɓi mulki shi ne cewa asibitocinmu sun zama ‘cibiyoyin tuntuɓa kawai’. A yau, da yawa daga cikin waɗannan asibitocin sun fi asibitocin tuntuɓa muni domin likitoci ƙalilan ne ma ake samun su a tuntuve su. Ba a gamsu da yanayin aiki a Nijeriya ba, dubbansu sun yi hijira zuwa ƙasashen waje domin yin aiki.

Ya zuwa watan Agustan 2022, adadin likitocin da Nojeriya ta horar da su da suka yi hijira zuwa Burtaniya kaɗai ya kai 10,096. A cikin wannan adadin, kimanin mutane 6,068 ne suka koma ƙasar Birtaniya tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari mulki a shekarar 2015. Waɗanda suka rage a ƙasar sukan shiga yajin aiki domin neman buƙatunsu na samun walwala.

Muna sake jaddada cewa, hanyar cigaba shi shi ne jagoranci nagari. Mun yi imanin cewa matsalolin Nijeriya za su iya daidaituwa kuma za a iya dawo da ƙasar kam hanya idan masu siyasa suka yi aiki don fansar al’umma; idan sun yi aiki don sake fasalinta.

Dole ne gwamnati ta fuskanci nauyin da ya rataya a wuyanta. Wajibi ne ’yan ƙasar su ƙara nuna kishin ƙasa, su kuma yi iya ƙoƙarinsu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Muna da kyakkyawan fata a shekarar 2023. Kuma ’yan Nijeriya su yi zaɓe cikin hikima a babban zaɓe mai zuwa. Wannan ita ce babbar hanyar da za mu iya dawo da martaba da ɗaukakarmu.