Ngigie ya shata daga da ASUU

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun karɓe ragamar sulhu da malaman jami’a da shugaba Buhari ya yi daga hannun Ministan Kwadago, Chris Ngige zuwa hannun Ministan Ilimi Adamu Adamu, aka daina ganin sunan Ngigen a tattaunawar shawo kan malaman su janye yajin aiki.

Yanzu dai wannan yajin aikin na borkono ya shiga wata na takwas kuma ya na daf da kai wa yin kunnen doki da wanda ƙungiyar ta yi a 2020 na tsawon wata tara kafin dawowa aiki. Duk wani mai yajin aiki in ba na ƙungiyar likitoci ba ne ba zai yi gogayya da ASUU ba.

A gaskiya ma yajin aikin ASUU ya sa in ma mutum ya ji sunan ƙungiyar baa bun da zai fara faɗo masa a zuciya sai tafiya yajin aiki. Ƙungiyar ta na da ƙarfi kuma kasancewar ta, ta malamai ce masu ’yanci da ra’ayi, ya sa ta na iya ɗaukar duk matakai don bin haƙƙin da ta ke magana ba tare da an bi ta bayan gida wajen yi ma ta zagon ƙasa ba.

A baya-bayan nan ma wasu ƙungiyoyi biyu masu alaƙa da jami’ar sun yi zama da ministan ilimi su ka janye yajin aikinsu amma hakan bai sa an koma karatu ba. Ina ma za a iya fara koyarwa ba malamai. Duk wani matakin da a ka ɗauka don dawowa aikin sai ya ci tura don akwai abun da gwamnati ba za ta so yi ba, hakanan su ma malaman akwai abun da ba za su amince da shi ba.

Tamkar ASUU na son yin amfani da wannan yajin ne don zama matakin warware dukkan matsalolin da a ka yi ta yarjejeniya ko tattaunawa a kan su tun 2009. Lamuran nan duk da akwai batun inganta albashi a ciki, amma za ka ji malaman na cewa batun gyara jami’o’in ne daga yadda wasun su, su ka zama kara zube.

Hakanan su na maganar samar da kuɗin aiyukan bincike da sauran abubuwan da ba lalle ne don more rayuwar malaman ba ne. Ko ma dai mene ne yara dai na gida ba sa samun karatu, yayin da waɗanda ke makarantu masu zaman kan su da waɗanda iyayensu, su ka tura ƙetare na cigaba da karatu kuma su samu gamawa a iya shekarun da a ka ƙayyade.

Hatta ɗaliban sun yi ta yunƙurin ganin an dawo karatun amma ina hakarsu ba cimma ruwa ba. Ambatar cewa su ’ya’yan talakawa ne ba ta taimaka malaman sun ji tausayin su ko gwamnati ta kawo mu su ɗauki ba. Duk barazanar rufe manyan hanyoyi ko ma’aikatar ilimi ba ta sauya komai ba don ASUU na cigaba da qara zafin borkonon ta ne.

Idan da ASUU ba tsayin daka ta yi ba, ai kuwa da ba za ta ɗaukaka ƙara ba bayan hukuncin kotun warware taƙaddamar ma’aikata da ya umurci malaman su koma bakin aiki. Shugaban ƙungiyar ta ASUU Farfesa Victor Emmanuel Osodeke ya caccaki jami’o’in jihohi da aka samu wasun su da niyyar buɗewa don dawowa karatu da cewa ’yan lakada-ka-was ne ko ba su da wata jajircewa ko kwarewar aiki tun da sun amince da batun komawa aiki gabanin warware taƙaddama da gwamnatin tarayya.

Jami’o’in jihohin sun buƙaci Osodeke ya janye kalaman sa amma zuwa yanzu ba mu ji inda ya yi hakan ba. Kullum a na ya sa ne ƙasa na ruftawa kan yajin aikin. Ka ga malamai na son a amince da manhajar biyan su da ta dace da su mai suna UTAS a takaice maimakon biya na bayyana da ake yi wa ma’aikatan Nijeriya wato IPPIS a taƙaice.

An fahimci cewa malaman na son su riƙa aiki a fiye da jami’a ɗaya da hakan kan sama musu ƙarin kuɗin shiga. Gwamnati ta dage sai da manhajar ta za ta riƙa biya kuma don fama targaɗe ta ce sam ba za ta biya malaman kuɗin albashin watannin da ba su aiki ba.

Ga wannan ɓangaren ƙungiyar ASUU ta ce ba za ta amince da hakan ba. Yaya za a fahimci mai gaskiya? Neman amsar wannan tambaya ya sa mutane sun rabu biyu ko ma uku. Akwai masu caccakar ASUU da cewa ba ta da wata hanya ta warware taƙaddama sai yajin aiki.

Wasu kuma na caccakar gwamnatin tarayya ne da cewa ta bar lamura sun rikice harkokin ilimi sun samu koma baya. Kazalika akwai masu tsayawa a ƙwarin kunya su na bugun jaki da taiki don samun ɓangarorin biyu su kai ga tsayawa a tsakiya don sulhu ko da kowane ɓangare bai cimma matsayar sa ba.

Ƙungiyoyin addini, sarakunan gargajiya da wasu masu faɗa a ji duk sun yi yunƙurin samar da sulhu a tsakanin sassan biyu amma lamarin ya ci tura. Da alamu ma wasu sun fara gajiyawa da wannan yanayi da ya zama yau fari gobe tsumma. Karatu a jami’o’in gwamnatin Nijeriya zai iya zama hanyar neman takardar shaida maimakon wajen samun ilimi mai inganci.

Idan malamai ba su kwantar da hankali ko ba su samu kwanciyar hankalin aiki ba ai ba za sui ya koyar da ɗalibai tsakani da Allah har a samu waɗanda nan gaba za su samu ƙwarewa wajen riqe ɓangarori mulki da sauran ayyukan ƙasa ba.

Duk lokacin da kasa ta shiga wannan yanayi nay aye ɗaliban da ba su iya biya allon su ba, to akwai babbar matsala da za ta yi barazanar maida hannun agogo baya. Nasarar ƙasa ta na da alaƙa ainun da yanayin ingancin tsarin ilmi da ta ke da shi kama daga firamare, sakandare har manyan makarantu masu ba da shaidar difloma da digiri har zuwa digirgir.

Duk kwazon ɗalibi ba zai nuna sosai ba a irin wannan yanayi na yajin aiki da faɗi tashin biyan kuɗin makaranta ko ɗawainiyar makaranta ba. Haƙiƙa akwai buƙatar ayyana dokar ta ɓaci kan karatun jami’a a Nijeriya.

Duk hanyar da gwamnati za ta bi wajen warware wannan damuwa ya dace ta yi ƙoƙari ta bi duk da ma an riga an makara; duk da shi gyara ba zai zama varna ba, kuma gyara kayanka ba zai zama sauke mu raba ba.

Gwamnatin Nijeriya ta dau matakin yi wa wasu ƙungiyoyin malaman jami’a biyu rajista don su zama ƙalubale ga ƙungiyar malamai ASUU da ke yajin aiki don amfani da hakan ya zama hanyar karya alkadarin ASUU da ta zama gagarabadau a yajin aiki a Nijeriya.

Ministan kwadago Chris Ngige ya yi wa ƙungiyoyin biyu rajista da su ka haɗa da ta malaman likitanci da magani NAMDA a takaice da kuma wata ta malamai mai suna CONUA a taƙaice. CONUA dai da ke hamayya da ASUU ta fara neman rajista ne tun 2018 kuma ƙungiyar da ke ƙarƙashin malami a jami’ar Obafemi Awolowo OAU Farfesa ‘Niyi Sunmonu na ƙauracewa duk yajin aikin da ASUU ta kira a baya. Shin ko ’yan wannan sabuwar ƙungiyar na da yawa in an kwatanta da ASUU kuma za ta zama kawar gwamnati a kullum in an samu irin wannan tangarɗar?

Minista Ngige ya ce ƙungiyoyin za su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ASUU kuma ya hore su, su haɗa kai da hukumomin jami’o’in.

Da alamu Ngige na son yankan ƙauna ne ga ASUU biyo bayan musayar kausasan kalamai tsakanin sa da shugaban ASUU Farfesa Osodeke a taron da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya kira don neman mafitar yajin aikin da ya shiga wata na takwas. A nan ya nuna Ngige ya sake ɓullowa ta wata kafa don ya cigaba da zama cikin hanyoyin fito na fito da ASUU.

Masu sharhi na ganin wannan ba zai sa lamuran koyarwa su dawo yadda a ke buƙata ba kuma zai iya ƙara rikita lamura ne kawai. A tarihi dai hukumomi kan samu nasarar rage tasirin jama’a masu fito na fito ta hanyar raba kansu.

Irin wannan yanayi ya so ya faru da qƙungiyar kwadago NLC lokacin da a farkon mulkin shugaba Buhari ya ƙara farashin litar fetur daga Naira 87 zuwa Naira 145. Bayan akasarin jama’a sun qi mara wa NLC baya don kyautata zato kan gwamnati za ta sharewa talakawa hawaye, ƙungiyar ta samu hamayya daga kishiya mai suna ULC a takaice.

Duk da daga bisani an daidaita amma har yanzu ƙarfin ƙungiyar kwadagon bai dawo kamar da can ba. Wato ma’ana ko da akwai ƙumbiya-ƙumbiya a can baya, duk da haka a kan ga tamkar NLC na tare da muradun talakawa kuma ta kan jajirce na ’yan kwanaki kafin a cimma sulhu ko matsaya.

Kammalawa;

Ya kamata kowa ya kawo ɗauki wajen samun janye yajin aikin ASUU don ɗalibai su koma makaranta. Ko yanzu a ka koma karatun ɗaliban sun riga sun cutu. Kaɗan ne daga ɗaliban masu kwazo kan yi bitar abun da a ka koya mu su a gida ko samun na gaba da su, su na yi mu su ƙarin karatu. Duk vangarorin biyu sai sun haƙura da wasu muradu ko matsayarsu don cimma maslaha.

Shugaba Buhari kansa ya yi amfani da lalama wajen roƙon malaman su koma aiki. Yin bayani filla-filla zai taimaka wajen fahimtar lamuran don wasu na cewa da gaske ne gwamnati ba ta da wadatattun kuɗin da za ta iya cimma buƙatun na ASUU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *