Wakilin Sin ya buƙaci a ƙara zurfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Jiya Jumma’a zaunannen wakilin ƙasar Sin dake MƊD Wang Hongbo ya bayyana cewa, gudanar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa, muhimmiyar dabara ce, a daidai lokacin da suke kokarin raya ƙasa bisa fifikonsu na musamman, don haka ƙasar Sin tana tsayawa tsayin daka domin goyon bayan haɗin gwiwar, kuma ta yi kira ga ƙasa da ƙasa da su haɗa kai domin kara zurfafa haɗin gwiwar.

Wang Hongbo ya faɗi haka ne yayin babban taron MƊD karo na 77 game da batun “sabuwar ajandar raya birane” da “raya harkokin ƙasa da ƙasa”, inda ya yi tsokaci cewa, ƙasar Sin tana ƙoƙari matuƙa kan aikin taimakawa sauran ƙasashe masu tasowa domin samun ci gaba tare, yayin da take ƙoƙarin raya kanta.

Haka kuma ƙasar Sin tana son haɗa kai da bangarori daban daban, domin hanzarta aikin aiwatar da ajandar samun ci gaba mai ɗorewa ta MƊD nan da shekarar 2030, ta yadda za a tabbatar da ci gaba mai ƙarfi da inganci ba tare da gurbata muhalli ba a faɗin duniya.

Jami’in ya ƙara da cewa, ya dace tsarin raya ƙasa na MƊD, ya martaba ikon mulki da jagoranci na ƙasashe masu tasowa, kuma kamata ya yi ya ba su goyon bayan da ya dace, yayin da suke ƙoƙarin raya ƙasashensu, musamman ma a ɓangarorin kawar da talauci, da samar da abinci da makamashi, da inganta tsarin tafiyar da harkokin ƙasa, da daga matsayin cuɗanya ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa

By Editor