Matawalle ya halasta tarurrukan siyasa, ya sake buɗe ƙananan hukumomi uku

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗage dokar haramta tarurrukan siyas da ta kafa a jihar.

Haka nan, ta janye dokar hana zirga-zirgar da ta kafa a yankunan ƙananan hukumomin Gummi da Anka da kuma Bukkuyum a jihar.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa labarai na Jihar, Ibrahim Dosara, ya fitar a Gusau ranar Litinin.

A cewar Dosara, gwamnati ta janye dokokin ne bayan gansuwar da ta yi da rahoton tsaron jihar da ta samu.

Daga nan, sanarwar ta buƙaci alummar jihar su ci gaba da gudanar da harkokinsu ta hanyar kiyaye doka da oda, kana su guji aikata duk wani abun da zai haifar da tashin-tashina.

Kwamishinan ya ce gwamnati ba za ta lamunci abin da zai haifar mata da cikas cikin zaman lafiyar da ta maido a jihar ba.

Kafin wannan lokaci, gwamnatin jihar ta ce, ta ɗauki matakin haramta tarurrukan siyasa da hana zirga-zirga a wasu yankunan jihar ne saboda dalilai na tsaro.

By Editor