Daga CMG HAUSA
A yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bikin buɗe taron wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniyar Ramsar kan yankuna masu dausayi ko COP14 a taƙaice.
Ana gudanar da taron ne daga yau Asabar 5 zuwa 13 ga watan Nuwanba, a birnin Wuhan na lardin Hubei dake yammacin tsakiyar ƙasar Sin, a matsayin wurin dake karɓar baƙuncin taron, da kuma makamancin taron dake gudana a Geneva na kasar Swizerland, dukkansu a zahiri da kuma ta kafar intanet.
Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
