Buhari da Paul Biya sun ƙaddamar da gadar da ta haɗa tsakanin iyakokin Nijeriya da Kamaru

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar gadar da aka gina a tsakanin iyakokin Nijeriya da ƙasar Kamaru.

An gina gadar ne a kan zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 19.3, wato dai-dai da Dalar Amurka miliyan 44.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai Buhari da takwaransa na ƙasar Kamaru, Paul Biya, suka haɗa gwiwa suka ƙaddamar da gadar ta Ekok/Mfum mai tsahon kilomita 1.5 da kuma tashar kasuwanci a bodar dukka a garin Mfun, na Jihar Kuros Ribas.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Ministan harkokin ƙasashen waje, Zubairu Dada, wanda ya bayyana cewa, wannan aikin gadar mai tsahon kilomita 1.5 zai ƙara ƙarfafa alaƙar tsakanin al’ummar ƙasashen biyu, kuma za ta qara kyautata rayuwarsu, ta cire matsalolin kasuwanci a tsakanin iyakokin ƙasashen biyu, sannan ta ƙara ƙarfafa tsaro a iyakokin biyu.

Sannan kuma ya ƙara da cewa, Hakazalika, wannan gada za ta sanya a samu alaƙoƙi masu ƙarfi a tsakanin ƙasashen Yammaci da Kudancin Afirka.

Sannan hakan zai qara sa a samun haɗin gwiwar qarfafa tsaro a tsakanin ƙasashen. Don daƙile ta’addaci da tsattsauran ra’ayi a yankunan.

Hakazalika a cewar sa, samar da gadar ya sanya farin ciki a zukatan mazauna yankunan. Sannan a cewar sa, wannan gadar ta zo a dai-dai lokacin buqatarta, saboda a kwanakin nan ne gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu a kan amincewa da yarjejeniyar cire hijabin kasuwanci a tsakanin ƙasashen Afirka (AfCFTA). Wanda ya yarje wa ƙasashen Afirka su yi kasuwanci tsakaninsu ba tare da shamaki ba.

Daga ƙarshe, shugaban ya ƙara da cewa, wannan tsarin ba makawa zai ƙara ƙarfafa alalar ƙasahen da suke mambobin ECOWAS.

Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban ƙasar Kamaru, wanda Ministan ƙasar na ayyukan al’umma, Emmanuel Nganuo Djours ya wakilta, ya bayyana cewa, wannan gada za ta ƙara qarfafa alaƙar cinikayya a tsakanin ƙasashen Nijeriya da Kamaru.

By Editor