Gwamnati ta ƙi biyan kishiyar ASUU duk da ƙin shiga yajin aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sabuwar ƙungiyar CONUA da aka yi wa rajista domin ta zama kishiyar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta koka kan rashin biyan albashin mambobin ƙungiyar duk da ƙin shiga yajin aikin da ƙungiyar ASUU ta dakatar.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya a ranar Talata, 4 ga Oktoba, 2022, ta yi rajistar ƙungiyoyin malaman jami’a guda biyu da suka haɗa da; ‘Congress of Nigerian Universities Academics’ (CONUA) da ‘National Association of Medical and Dental Academic’ (NAMDA).

An yi rajistar ƙungiyoyin biyu kafin ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta shafe watanni takwas tana yi a ranar 14 ga Oktoba, 2022.

Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi, Chris Ngige, wanda ya yi wa ƙungiyoyin rijista a madadin gwamnati ya bayyana cewa ƙungiyoyin biyu za su kasance tare da ASUU, ya ƙara da cewa, ƙungiyoyin biyu za su cigaba da bibiyar haƙƙi da gata da aka bai wa sauran ƙungiyoyin ilimi a fannin ilimi.

Yayin da ƙungiyar ASUU ta cigaba da yajin aiki, gwamnatin tarayya ta dage kan aiwatar da manufar ‘Ba Aiki, Ba Biya’, a lokacin da malaman jami’o’in ba su yi aiki ba, wanda sabbin masu rajistar suka ce ba sa cikin yajin aikin.

Sai dai al’amura sun ɗauki wani sabon salo a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, 3 ga watan Nuwamba, 2022, inda aka tattaro cewa gwamnati ta biya malaman jami’o’in albashi na rabin wata ne kawai.

An yi ikirarin cewa yayin da gwamnati ta ba da umarnin biyan albashin watanni bakwai na albashin malaman lafiya, har yanzu mambobin CONUA ba su sami wani bayani game da biyansu ba.

Da ya ke tabbatar wa manema labarai hakan, sakataren CONUA na ƙasa, Dakta Henry Oripeloye, ya ce, babu wani ɗan ƙungiyarsa da aka biya ko sisi.