ASUU ta kira taron gaggawa kan shiga sabon yajin aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Jami’’o’i (ASUU) ta kira zaman gaggawa na Majalisar Zartarwarta don yanke shawara kan shiga sabon yajin aiki.

ASUU ta kiran zaman gaggawan ne sakamakon rabin albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya malaman jami’a bayan sun janye yajin aiki.

Wani mamba a kwamitin zartarwar ASUU ya ce, mambobin ƙungiyar sun fusata da yanke albashin nasu da suke zargin Ministan Ƙwadago, Chris Ngige da yi.

Wani jami’in ƙungiyar ya shaida wa manema labarai cewa, majiya mai tushe ce ta sanar da su cewa ministan ne ya ba da umarnin yanke albashin da aka biya su a Oktoba.

“Ina tabbatar maku da cewa NEC ɗin ASUU NEC zai yi zama ranar Litinin 7 ga Nuwamba domin ɗaukar matsaya game da shiga sabon yajin aiki, saboda rabin albashin da aka biya mu a Oktoba.

“Sassann ƙungiyar sun fusata da abin da Gwamnatin Tarayya ta yi, don haka ƙungiyar za ta yanke shawara a ranar 7 ga watan Nuwamba,” inji shi.