Daga CMG HAUSA
Jiya Litinin, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Amurka Joe Biden, a tsibitin Bali na ƙasar Indonesiya.
Bayan ganawar ta su, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya yi ƙarin bayani ga kafofin watsa labarai game da ganawar shugabannin biyu.
Wang Yi ya ce, ganawar shugabannin biyu na da muhimmiyar maana, domin wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasar Sin da na Amurka suka yi ganawa fuska ta fuska cikin shekaru 3 da suka gabata, kuma karo na farko da shugabannin biyu suka gana da juna fuska ta fuska, bayan shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya kama aiki.
Kaza lika, wannan shi ne karo na farko, da shugabannin koli na ƙasar Sin da na Amurka suka yi muamala, bayan sun kammala muhimman taruka cikin ƙasashensu.
Game da batun dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar shugabannin biyu, an tabbatar da cewa, za a magance taɓarɓarewar dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu, yayin da ake neman wata hanyar da ta dace ta daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.
Kuma, za a tattauna cikin haɗin gwiwa, domin fidda manufar daidaita dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Sannan, an fara yunkurin aiwatar da raayin shugabannin biyu, ta yadda za a daidaita dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu cikin yanayin zaman karko.
Haka kuma, a yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun mai da hankali kan batun lardin Taiwan na ƙasar Sin.
Wang Yi ya ce, ƙasar Sin na fatan Amurka za ta aiwatar da matakai masu nasaba da hakan, kamar yadda ta bayyana, da kuma bin manufar ƙasar Sin ƙasa ɗaya tak a duniya”, da sanarwar haɗin gwiwa guda uku da ƙasar Sin da Amurka suka ƙulla, da kauce wa ɓata yanayin lardin Taiwan.
Dangane da wannan batu, shugaba Biden ya ce, ƙasar Amurka tana tsayawa tsayin daka kan manufar ƙasar Sin ƙasa ɗaya tak a duniya, kuma ba ta goyon bayan ɓallewar yankin Taiwan daga ƙasar Sin, kana ƙasar Amurka ba ta da burin hana bunƙasuwar ƙasar Sin ta hanyar rura wutar batun Taiwan.
Dangane da ci gaban da ƙasashen biyu suka samu a fannin haɓaka hadin gwiwa bisa fannoni daban daban, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar shugabannin biyu, shugaba Xi Jinping ya ce, bai kamata a dakatar da aikin raya dangantaka a tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Amurka sakamakon bambancinsu ba, kuma ya kamata ƙasashen biyu su dukufa wajen tsawaita jerin haɗin gwiwar dake tsakaninsu.
Bugu da ƙari, a yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana matsayin ƙasar Sin kan wasu batutuwan dake janyo hankulan ƙasar Amurka, da ma sauran ƙasashen duniya.
Shugabannin biyu, sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan dake shafar ƙasar Ukraine, da batun nukiliyar zirin Koriya da dai sauransu.
Mai Fassarawa: Maryam Yang
