Ganduje zai rattaba hannu kan zartar da hukuncin kisan Abduljabbar – Kwamishina

Spread the love

Daga WAKILINMU

Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Lawan Musa, ya bayyana cewa, a shirye Gwamna Abdullahi Ganduje yake ya rattaba hannu kan zartar da hukuncin kisan da kotu ta yanke wa Abduljabbar Nasiru-Kabara.

A ranar Alhamis Kotun Shari’a ta Kano ta yanke wa Malamin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta same shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Kwamishinan ya shaida wa jaridar Daily Trust a ranar Alhamis cewa, Ganduje na bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da ba a yi wa doka karan tsaye a jihar.

Ya ce, gwamnatin jihar ce ta maka Abduljabbar a kotu, wanda hakan ke nuni da babu wanda ya fi ƙarfin doka a jihar.

“Babu wanda zai take doka ba tare da an ɗauki matakin da ya dace a kansa ba.

“Mu muka kai shi kotu sannan muka ba shi duka abin da yake buƙata don kare kansa, ga shi yau Allah Ya sa kotu ta ga muna da gaskiya ta kuma yanke hukuncin da ya dace a kansa,” in ji Kwamishina.

Ya ce, da yake akwai matakai masu yawa da akan bi kafin komai ya kammala, amma da zarar takardar izinin zartar da hukuncin ta zo gaban Ganduje zai rattaba hannu ba tare da ɓata lokaci ba.

Haka nan, Musa ya ce matsayar Gwamnan ba ta sauya ba kan batun kisan yarinyar nan Hanifa.

By Editor