Daga MUHAMMAD SANUSI a Gusau
A ƙoƙarinta na ganin an gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin lumana, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin CP Kolo Yusuf, ta tabbatar wa al’umma cewa an samar da matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Muhammad Shehu.
Sanarwar ta ce, an girke jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da dama a majami’u da sauran wuraren shakatawa domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali a jihar.
“Don ƙara karfafa ayyukan tsaro da ake da su, Kwamishinan ‘yan sandan ya fara sintiri a kan manyan tituna, wanda ya taso daga titin Gusau-Mafara-Sokoto,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa, an gunanar da sintirin ne da nufin tabbatar da tsaro da kuma lafiyar matafiya da sauran masu amfani da hanyoyin.
CP ya kuma baiwa kwamandojin yankunanan ƙananan hukumomi goma 14 dake jihar, umarnin gudanar da aiki da dabaru iri ɗaya a yankunansu domin tabbatar da tsaron al’umma.
Rundunar ta gargaɗi jama’a ban da sayar da kayan wasan wuta a cikin jihar don, haka aka shawarci iyaye da su sanya ido a unguwannin su don tabbatar da yaransu sun kasance masu bin doka da oda.
“Masu amfani da tituna su yi taka tsantsan yayin tuƙi, kuma su bi duka ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa tare da bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro kafin, lokacin da kuma bayan bikin.
“Kwamishanan ‘yan sanda a madadin rundunar, yana taya ɗaukacin al’ummar jihar da mazauna jihar musamman mabiya addinin Kirista murnar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
“Ya kuma buƙace su da su yi amfani da lokacin don aiwatar da addu’ar zaman lafiya da tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya,” in ji sanarwar.
