Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta yaye ɗalibai 100 a Nasarawa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin ta makon jiya, Kwalejin Nazarin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta yi bikin yaye wasu ɗalibanta da suka kammala karatu a wasu sassa biyu, wato sashen nazarin lafiyar ido da na nazarin kimiyyar abinci, wato ‘Dietetics Technician’ a Turance.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban kwalejin, Alh Dokta Sulaiman Abdullahi, ya ce wannan shi ne karo na biyu da makarantar ke yaye ɗalibai a waɗannan sassa.

Ya ce tarin nasarorin da kwalejin ta samu ya sa makarantar ta zamo ɗaya daga cikin makarantun nazarin kiwon lafiya ukun da ke kan gaba a faɗin ƙasa.

Abdullahi ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yaba wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abdullahi Sule dangane da ƙoƙarin da take yi wajen bunƙasa kwalejin.

Ya ƙara da cewa, nan ba da daɗewa ba za a ɗaga darajar kwalejin domin nazarin kwasa-kwasai a matakin digiri.

Da yake yi wa wakilinmu qarin haske, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kwalejin, Adamu A. Musa, ya ce aƙalla ɗalibai 100 ne aka yaye a wannan karon.

Kuma ƙungiyoyin ƙwararru a sassan sun shigo sun rantsar da su tare da miƙa musu lasisin zama cikakkun mambobinsu.

Sashe na ɗaliban da aka yaye

Ya ce ana sa ran ɗaliban da aka yayen su tafi cibiyoyin kiwon lafiya zaɓin ransu, inda za su yi zama a can na shekara ɗaya don sanin makamar aiki.

Dukkan waɗanda suka yi jawabi a wajen taron, sun yi wa kwalejin da ma ɗaliban da lamarin ya shafa fatan alheri, tare da kira ga ɗaliban kan su zama jakadu nagari a duk inda suka tsinci kansu.

Taron ya gudana ne a babnan zauren taro na kwalejin da ke Sabon Gari, Keffi, kuma ya samu mahalarta daga ciki da wajen Jihar Nasarawa.

By Editor