Za a yi sanyi mai tsanani da hazo mai yawa na tsawon kwanaki 3 a Kano da Jigawa – NiMET

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar Kula da Yanayi da Annoba ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen samun yanayi mai yawan hazo tun daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a wasu wurare a faɗin ƙasar nan.

NiMet ta saki bayanin wannan hasashen yanayin nata ne a a Abuja, inda aka bayyana cewa, za a samu hazo mai yawa sosai a wasu ɓangarori na Arewacin Nijeriya na kwana uku.

Ɓangarorin da abin ya shafa sun haɗa da jihohin Yobe, Kano, Katsina da kuma Jigawa.

Wannan yanayi zai fara daga juma’a ne zuwa Lahadi. Sauran jihohin da suke a yankunan Arewa ta tsakiya kuma za a samu matsakaici hazo da ƙura saisa-saisa.

Haka a ranar Lahadi ma a ɓangarorin Kano da Jigawa, da Yobe da Katsina shi ma za a samu irin wannan yanayin, sai dai ɗan ƙarin kaɗan na yawan hazon.

A don haka, hukumar ta NiMET take kira ga al’umma da su ɗauki matakan kare kansu daga wannan yanayi. Saboda ƙura da za ta gurbata yanayi.

Hakazalika, mutane masu cututtukan da suka shafi hanyoyin numfashi su katange kansu daga yanayin mai cike da ƙura don kiyaye lafiyarsu.

Haka da dararen ranakun da ma a shirya samun sanyi mai tsanani. Don haka a cewar hukumar, a sunkufe ƙananan yara da kayayyakin sanyi, sannan masu kula da tashin jiragen sama ana shawararsu da su dinga tuntubar rahotannin hasashen yanayi na NiMET don tsara yadda za su tafiyar da ayyukansu.

By Editor