Daga IBRAHIM HAMISU, Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu matasa su 61 da ta cafke bisa zargin su da ayyukan ta’addanci ta hanyar ƙwacen wayoyin mutane a ranar Larabar makon nan.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, SP Abdullahi Haruna, ya fitar ranar Alhamis.
Kazalika, sanarwar ta ce, an cafke matasan ne ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi yayin gudanar da taron bada tutar ‘yan takarar jam’iyyar APC a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.
