Diezani ta kama hanyar ƙwato kadarorinta

Spread the love

Daga WAKILINMU

Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, ta kama hanyar maido da kadarorinta da gwamnati ta ƙwace

Ta yi hakan ne ta hanyar shigar da ƙara inda ta buƙaci wata Babbar Kotun Tarayya da ta janye umarnin da ta bai wa Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC) na ƙwace mata kadarorinta.

Ta shigar da buƙatar ce tana mai neman Kotun ta dakatar da EFCC daga sayar da kadarorin da ta ƙwace mata.

“An yaudari kotunan ne wajen ba da umarnin kwace kadarorinta ta hanyar danniya ko kuma rashin bayyana gaskiyar abin ga duniya,” in ji ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito EFCC na shirin sayar da kadarorin Diezani da ta ƙwace ga mabuƙata daga ranar 9 ga Janairu kamar yadda yake ƙunshe cikin sanarwar da hukumar ta fitar.

Wannan ya biyo bayan nasarar da EFCC ɗin ta samu ne a kotu a lokuta daban-daban kan ta yi gwanjon kadarorin da ta ƙwace a hannun tsohuwar Ministar.

Sai dai kuma, a ƙarar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/21/2023 da kuma kwanan wata 6 ga Janairu ta hannun lauyanta, Mike Ozekhome, Diezani ta buƙaci alƙalin kotun Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ba da umarnin dawo mata da kadarorinta.

Ta ba da hujjar cewa umarnin da aka bai wa EFFC an yi hakan ne ba tare da wani hurumi ba.

Ta ce ba a yi mata adalci ba a duk shari’o’in da suka kai ga ba da umarnin ƙwace mata kadarori.

Ƙarar da Diezani ta shigar cike take da zargin ba a yi mata adalci ba, dalilin ke nan da ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Sai dai wani jami’in EFCC da ya samu ganin takardar ƙarar da tsohuwar ministar ta shigar, ya faɗa wa NAN cewa galibin zargin da Diezani ta yi ba gaskiya ba ne.

A nata ɓangaren, EFCC ta nemi kotu da ta yi watsi da ƙarar tsohuwar ministar.

By Editor