*Ya ce, salon yaƙi da cin hanci da bunƙasa arziki ne
*Mun daidaici wannan lokacin ne da gayya, inji shi
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa kan yadda ’yan Nijeriya ke shan azaba sakamakon canjin fasalin manyan takardun Naira, yana mai bayyana cewa, shan azabar ya zama wajibi matuƙar Nijeriya ta na son ta kawo ƙarshen matsalar annobar cin hanci da rashawa da ta yi kaka-gida a ƙasar da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Kalaman na Shugaban Ƙasa sun fito ne daga bakin Ministar Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed, bayan kammala zaman Majalisar Zartarwar Tarayya a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja jiya Alhamis, 2 ga Fabrairu, 2023, inda ta ƙara da cewa, Shugaba Buhari ya yi matuƙar damuwa da halin da ’yan Nijeriya ke ciki, amma ta nanata cewa, hakan ya zama wajibi, domin yana faruwa ne sakamakon canjin da ake ƙoƙarin samarwa.
Ministar ta ƙara da cewa, wannan manufa an daidaici lokacin da ya dace ne wajen aiwatar da ita. Don haka tana da nata alherin na wawashe ɗimbin dukiyar da aka sace aka danƙare su guri guda.
Idan dai za a iya tunawa, gabanin ƙarewar shekarar bara ta 2022, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sauya fasalin takardun Naira na 1,000 da 500 da 200, inda ya sanya wa’adin ranar 31 ga Janairu, 2023, a matsayin ranar sa tsofaffin takardun kuɗin za su daina aiki, amma bayan matsin lamba daga sassa daban-daban a ƙasar, ya ƙara wa’adin lokacin zuwa ranar 10 ga Fabrairu, wa’adin da har yanzu Majalisar Dokoki ta Nijeriya ta qi amincewa da shi.
A binciken da Blueprint Manhaja ta gudanar, Babbar damuwar ’yan Nijeriya ita ce, yadda sababbin takardun kuɗin suka yi qaranci, sannan kuma ‘network’ na aikawa da kuɗaɗen ta hanyar intanet ya jagule, bugu da ƙari, a yankunan karkara akwai matsalar rashin bankuna da kuma wayewa kan harkokin bankin intanet.
