Daga BASHIR ISAH
Gwamnanonin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara sun maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Ƙoli kan batun canjin kuɗi.
Sun kai ƙara kotun ne inda suke neman kotu ta hana Gwamnatin aiwatar da cikakkun matakan da ta ɗauka dangane da sabbin kuɗaɗen.
Ƙarar da suka shigar ta hannun lauyansu, AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN), gwannonin sun buƙaci Kotun Ƙoli da ta ba ikon dakatar dakatar da Gwamnatin Tarayya ko CBN da sauran bankuna dakatar da su daga hana kawo ƙarshen tsoffin takardun Naira na 200 da 500 da 1000.
Waɗanda suka shigar da ƙara sun haɗa da Manyan Lauyoyi uku da kwamishinonin shari’a na jihohin uku, yayin da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), shi ne kaxai wanda ake ƙara.
Masu ƙarar sun ce tun bayan da aka ba da sanarwar sabbin takardun Naira ake fuskantar ƙarancin Nairar a jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara.
Alhali a’ummar jihohin sun maida tsoffin takardun na Naira banki kamar yadda aka buƙace su, amma kuma samun sabbin ya ci tura wanda hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali.
