*Yadda fafatawar neman shugabancin Majalisar Dokokin Nijeriya yake ƙamari
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Makonni ƙalilan kafin a rantsar da Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10, a karon farko jam’iyyun adawa a ƙasar su na ƙara samun ƙwarin gwiwar yin yunƙurin naɗa shugabanci a majalisar, musamman ma Majalisar Wakilai, wacce yawansu ya ɗari na jam’iyya mai mulki, wato APC.
To, sai dai kuma ita ma APC ɗin tana cigaba da jan ɗamara kan sai ta ga abinda ya ture wa buzu naɗi.
A karon farko dai a tarihin Nijeriya an zaɓi mambobin jam’iyyun adawa har sun fi na jam’iyya mai mulki bayan kammala babban zaɓen 2023, inda jam’iyyar APC mai mulki ke da zavavvun mambobi guda 175, yayin da sauran jam’iyyun ke da 182, wato bambancin kujeru bakwai kenan, kuma har yanzu ba a kammala zaɓuka a wasu ƙalilan ɗin kujeru ba.
Wannan ya haifar da shakku kan ko zai iya yiwuwa APC ta iya kafa shugabancin Majalisar Wakilai. Jaddawalin wakilan majalisar bayan kammala zaɓen cike gurbi ya nuna cewa, APC tana da 175, PDP tana da 118, LP tana da 35, NNPP tana da 19, APGA ta na da biyar, yayin da SDP da ADC ke guda biyu kowacce, ita kuma YPP tana da guda ɗaya, yayin da ake jiran guda uku, waɗanda ba a samu sakamakonsu ba.
Idan za a iya tunawa, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa, su na kan hanyar da za a bi wajen ganin an cimma matsaya kan shugabancin Majalisar Wakilai ta 10.
Sai dai jam’iyyun adawa sun numa sam ba haka ba, kamar yadda suka bayyana shirin tsayar da ɗan takarar Kakakin Majalisar Wakilai da mataimakinsa.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na Ƙasa a ranar Laraba a Abuja, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce, jam’iyyar za ta tuntuɓi juna, musamman da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, kafin ta cimma matsaya kan raba muƙamai ga yankunan siyasa na ƙasa a jagorancin majalisa.
Da aka tambaye shi game da tsarin shiyya-shiyya da jam’iyyar ta ƙulla, Adamu ya ce, “Ba abin da taron na yau yake nufi ba kenan.”
Shi ma da yake tabbatar da matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa kan sakamakon taron, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Barista Felix Morka ya ce, taron na Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar (NWC) ya duba wasu al’amura na cikin gida na daban ne, waɗanda suka haɗa da shirin wani ɗan jam’iyyar NWC na maka shugabannin jam’iyyar a kotu.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a yankin arewa maso yamma, Salihu Moh Lukman, ya maka shugaban jam’iyyar na ƙasa da kuma sakatariyar jam’iyyar a gaban kotu bisa zargin karya kundin tsarin mulki.
Lukman na roƙon kotu da ta tilasta wa hukumar NWC da Adamu ke jagoranta ta kira taro na hukumomin jam’iyyar tare da yin asusu na kuɗi.
Amma da yake magana kan lamarin, kakakin jam’iyyar APC ya ce, “Daga cikin dukkan batutuwan da aka tattauna a taron, mun duba wasu al’amura na cikin gida da wani abokin aikinsa (Lukman) wanda ya bayyana damuwarsa kan wani abu da yake ganin ya kamata jam’iyyar ta kasance akai
“Mun yi shawara gaba ɗaya game da shi. Kuma kamar yadda muke magana, kwamitin da aka kafa don kammala wannan tattaunawa yana ci gaba da gudana a yanzu. Don haka, akwai taron da ke gudana wanda ya kamata in kasance cikinsa don gyara wannan tattaunawar da bayar da shawarwari na ƙarshe kan wannan batu.
“Amma na yi farin cikin bayar da rahoto kamar yadda shugaban ya bayyana. Jam’iyyar ta tsaya tsayin-daka da jagoranci na gari da shugabanmu na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu ke yi. Kuma duk muna tare da shi.”
to, sai dai kuma, a yayin da APC ke cikin wancan ruɗani, jam’iyyun adawa da suka haɗa da PDP, LP, NNPP, YPP, SDP da APGA sun kammala shirin tsayar da ’yan takarar kujerar Kakakin Majalisar Wakilai da mataimakinsa na majalisar wakilai ta 10 tare da yanke shawarar shiga takarar shugaban majalisar.
Ƙungiyoyin tsirarun jam’iyyun sun kuma ce suna shirin kafa wani kwamiti mai mutum 11 da zai taimaka wajen sa ido a tsakanin su na ɗan takarar da zai tsaya takara a zaɓen.
A al’adance, jam’iyyar da ke da rinjayen zaɓaɓɓun mambobinta, ta kan samar da shugabannin majalisun biyu na majalisun tarayya.
