Mutane takwas sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Bayanai daga garin Yawuri da ke Jihar Kebbi sun bayyana cewa aƙalla mutane takwas ne suka rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a garin Yawuri farkon makon nan.

Wani jami’in hukumar kula da harkokin ruwa ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, jirgin mai ɗauke da mutane kimanin 30 da ya taso daga Agwara da ke jihar Neja ya ɗauko fasinja daga ƙauyukan Gebbe, Kasabo da kuma Mago maƙare da buhunan abinci kimanin tamanin da kaya da dabbobi daga jihar Neja zuwa Yawuri wajen cin kasuwa inda ya kife.

Shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Yauri, Honarabul Bala Muhammad Gagga, ya tabbatar da hatsarin jirgin inda ya ce an yi jana’izar waɗanda suka rasu kuma ana cigaba da neman sauran mutane cikin ruwan.

Malam Muhammed Sani da abin ya faru a gaban idonsa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho da cewa iska mai ƙarfin gaske ce ta ɗauko igiyar ruwa sai jirgin ya soma tangal-tangal har ya nutse inda daga nan kafin zuwan hukumomi tuni mutane suka shiga ƙananan kwale-kwale suka soma kai agaji.

Ya ƙara da cewa har zuwa cikin daren Litinin dai an lalubo gawarwaki takwas na waɗanda suka rasu da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara.

Ya kuma bayyana cewa an samu nasarar ceto wata mata da goyonta da kuma wanɗansu mutane bakwai sun tsira da ransu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar mulki ta Yawuri Honarabul Bala Muhammad Gagga, Area Commander, DPO da Ubandoma, wakilin HYPHADEC duk sun isa bakin ruwan.

Al’umma masu tofa albarkacin bakunansu sun ta’allaƙa hatsarin da yin lodin da ya fi ƙarfin jirgin inda suka ce aƙalla akwai kimanin buhunan abinci tamanin da dabbobi da kuma kayayyaki da jirgin ya xauko, da aka ce direban jirgin saboda ganin guguwar da ke kaɗawa sai da ya tsaya  a wata gaba ya nemi mutane su rage amma sai suka yi biris da maganar sa.

Gwaman jihar Kebbi Alhaji Nasir Idris ya jajentawa iyalan waɗanda suka rasu da kuma Masarautar Yawuri inda ya bayyana hatsarin a matsayin wata annoba.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi za ta ɗauki matakan rage hatsarin kwale-kwale da rasa rayuka ta hanyar haɗa hannu da hukumomin da ke kulawa da harkokin zirga-zirgar ruwa inda ya ce za a saka dokar taqaita yawan adadin kaya da mutane da za a iya ɗauka, tare da tabbatar da an tanadi rigunan hana nutsewa ga kowane fasinja.

Haka zalika Gwamna Nasir ya bayar da kyautar Naira milliyan takwas ga iyalan marigayan da kuma milliyan biyar ga masarautar.

Mai Martaba Sarkin Yawuri Dr Zayyanu Abdullahi ya yaba wa gwamna bisa ga kulawar da ya ke yi ga alu’ummar jihar na kai ƙafarsa a duk inda wani al’amari ya faru ko na murna ko kuma akasin haka.

Ya kuma ƙaryata maganganun da ‘yan kafafen yaɗa labarai na zamani da yaɗa cewa mutane 30 ne suka rasu inda ya bayyana cewa bakiɗaya mutane 17 ne ke cikin jirgin kuma gawarwaki takwas ne aka tsamo har yanzu masu aikin ceto na cigaba da neman sauran.

By Editor