Masu hikimar magana su na cewa duk wadatar mutum za a iya taimakon sa, haka duk talaucin mutum zai iya taimakon wani. Shi taimako ya danganta daga mutum zuwa wanda zai ma taimakon wani addu’a ce za a taya masa.
Wani kuɗi ne, buƙatar wani kuma abin yi ne, buƙatar duka dai mu lura da yadda sabon minista na ɓangaren labarai Alhni Muhammed Idris Malagi ya zamo mai ayukka da yawa, kai ka ce baya ga minista a ɓangaren labarai da kuma wayar da kai, tamkar shi ne mai magana a madadin shugaban ƙasa Tinubu.
Duk wanda ya ke sauraren kafafe na yaɗa labarai na gida da waje zai tabbatar da cewa wancen minista na labarai ya zamo na daban ta fuskar wayar da kan jama’a ga kuma sauƙin hali da sauraren jama’a, don haka na ga dacewa duk ma su kishin ƙasa mu haɗu mu taimaki mutane irin su Muhammed Idris Malagi da addu’ar alkhairi. Allah ka iya mai ya amfanar da mu a wannan matsayi na minista.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa a Katsina. 07066434519/ 08080140820.
