Son zuciya da ɓacin zuciya sai Nijeriya

Spread the love

Shugabanni suna son su rayu su arzuta cikin walwala, amma basu son talaka ya rayu ya arzuta, shi yasa suke son haifar da ruɗani a fannin tattalin arziki a ƙasa.

Allah Ya yi ruwan man fetur a Nijeriya, ya yi albarkar noma da albarkatun ma’adinai da mashigin ruwa da iyakokin ƙasa masu albarka, da kasuwa kala-kala da arzikin jama’a. Amma ƙarfi da yaji ake son a lalata ƙasar a jefata cilkin ruɗani saboda son zuciyar mutane ƙalilan.

Saboda duk inda talauci da yaudara da rashin iya jagoranci suka yi katutu dole hassada da rashin martaba juna su shigo daga nan kuma sai rashin haquri da qin juna su ti tasiri a nemi raba ƙasar. Yin ko oho da rayuwar talaka a Nijeriya hatsari ne ga zaman lafiyar ƙasa. Allah ya bamu mafita ya ceci bayinsa daga masu mummunar manufa.

Daga Muazu Hardawa, Edita Jaridar Alheri a Bauchi. 08062333065.

By Editor