IPAC ta yaba wa gwamna Sule dangane da ayyukan cigaba a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Wata ƙungiyar haɗakar jam’iyyun siyasa mai zaman kanta da ake kira ‘Inter-party advisory committee’ wato IPAC a Turance na ƙasa ta yaba wa Gwamnan Jihar Nasarwa Injiniya Abdullahi Sule dangane da muhimman ayyukan cigaba da gwamnatin sa ke gudanarwa a jihar kawo yanzu.

Shugaban kwamitin IPAC ɗin Yabati Sani ne ya bayyana haka wa manema labarai a lokacin wani ziyarar duba ayuka na musamman da ƙungiyar ke gudanar a duka jihohin ƙasar nan wadda ta faro da jihar ta Nasarawa.

Ya ce ba shakka ayayin ziyarar duba ayyukan tawagar tasu ta gano wasu muhimman ayukan cigaba da dama da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta gudanar da suka haɗa da babban ginin kwana na gwamnan mallakar gwamnatin jihar da ke Abuja da babban tashar mota da ke Maraba irin na zamani a jihar da kwalejin kiwon lafiya dake garin Keffi da dai sauran su inda ta gano cewa gwamnan ya tsara su ne irin ta zamani kuma ta kashe maƙuden kuɗaɗe wajen gina su.

A cewar Yabati Sani tabbas gwamna Abdullahi Sule ya cancanci yabo a waɗannan fannoni inda ya buƙaci sauran gwamnonin ƙasar nan duka suyi koyi da shi.

Yabati ya kuma sanar cewa ƙungiyar da ke zaman kanta ta yanke shawarar kai ziyarar duba ayyuka a duka jihohin ƙasar nan ne don tabbatar gwamnonin suna cika alqawura da suka yi wa jama’ar su a lokutan kamfen da sauran su inda ya ƙara da cewa, ƙungiyar ba tana yin haka don cin zarafin wani ko wata bane amma don tabbatar da ana yi wa talakawa aldalci ne ta wajen samar musu da abubuwar more rayuwa kamar yadda ya dace.

Shima a nasa ɓangaren wanda ya jagoranci ɓangaren gwamnatin jihar a ziyarar duba ayukan cigaban wato mai taimaka wa gwamnan a fannin jama’a mista Peter Ahemba ya bayyana wa wakilin mu cewa a yayin ziyarar sun nuna wa tawagar IPAC ɗin wasu ayuka ne kadan daga cikin dinbin ayyukan cigaba da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ke cigaba da aiwatar wa al’ummar jihar inda yace ba shakka tawagar IPAC ɗin sun yaba wa gwamnan matuƙa a yayin ziyarar.

Daganan sai Peter Ahemba yayi amfani da damar inda ya buaaci al’ummar jihar ta Nasarawa baki ɗaya su cigaba da bai wa gwamnatin Abdullahi Sule cikakken goyon baya don bashi damar cigaba da samar musu da ɗimbin nasarorin.

By Editor