Daga BASHIR ISAH
Mataimakin Gwnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya bayyana aniyarsa ta neman shiga takarar gwamnan jihar ya zuwa 2024.
Ya ce zai tsaya takarar ne a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, tare da cewa, babu abin da zai hana shi neman kujerar gwamnan jihar.
Shaibu ya bayyana aniyyar tasa ce da safiyar ranar Litinin a cibiyar Biohop Kelly Centre da ke Benin City, babban jihar.
Da yake yi wa dandazon masoyansa jawabi, Shaibu ya ce a matsayinsa na ɗan asalin jihar wanda kuma ya san ciwon al’ummar jihar, zai nemi shugabancin jihar ne don cigabanta da ma al’ummarta baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, babu abin da zai dakatar da shiga daga takarar gwamnan jihar a zaɓen 2024 mai zuwa.
Kazalika, ya ce ya yi aiki tare da Gwamna Godwin Obaseki na tsawon shekara bakwai da suka shuɗe wajen aza tubalan gina Jihar.
Don haka ya yi kira ga al’ummar jihar da su mara masa baya don cimma nasarar zama Gwamnan Edo na gaba.
