Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin baiwa da ya siya (3)

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba.

Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da mata huɗu, sai a gidan wanda uwata take zaune wurin sa ya ce, wai ni baiwa ce, kuma mutumin ne ya siye ni daga hannunsa. Kuma zan zauna da shi matsayin matarshi.

Nan na zauna cikin tsangwama, ba mai shiga sha’anina daga matanshi ko dangi, suna ƙyama ta, ko shi kamar yana voye ni a wajen mutane, bai cika faɗa wa mutane ko ni wacce ce ba. Haka na haihi ɗiya har guda huɗu, sannan kuma Ina zuwa makaranta ta Allah, ana mana karatun Ƙur’ani da sauransu. To shi ne kwanaki mallam yake bayani sai ya yi maganar babu bayi, ɗiya ne ake ta saye, ana zaman zina da su.

AMSA:

A wani bayani na wani malami, ya bayyana mas’alar bayi a wannan zamani da bayin ƙarfi da yaji, inda ya kira su da ‘bayin zamani’. Su waɗannan bayi suna samuwa ne daga kalmar aikatau. Za a tafi ƙasashe masu fama da talauci, a ɗauko yara da sunan za a kai su aiki wasu ƙasashen, za su samu albashin da har za su dinga yin aike gida.

Yayin da aka kai su, sai su tarar da babu kaso mafi rinjaye na gaskiya a zancen da aka faɗa masu kafin a ɗauko su. Za a ajiye su a wulaƙantacen ɗaki, a dinga sanya su ayyukan bauta, sannan a ba su ɗan abinda bai kai ya kawo ba na daga albashi.

A irin wannan ne ake samun wasu idan sun tafi da yaran sai su sayar da su a matsayin bayi ga waɗanda aka ce za su yi wa aiki. Ta wannan ne a idon duniya su masu aiki ne, sai dai a ƙarƙashin ƙasa an yi cinikinsu har an biya.

A cikin wannan yanayi ne, ake samun wasu daga cikin waɗanda suka siye su, su mayar da su mallakinsu, suna tursasa kansu gare su ta fuskar kwanciya, yayin da waɗansu ke azabtar da su, azaba mai yawa, duk da sunan sun siye su a matsayin bayi.

A Musulunci, wannan kusanta da za su yi masu, duk da cewa sun zuba kuɗi sun siye su ne, hukuncin sa daidai yake da na wanda ya yi fyaɗe, domin bai amince da irin wannan cini da sunan bauta ba.

Idan za ki tambaye ni, halascin bayi a wannan zamani a inda fuskata ta karkata, zan iya cewa babu bayi, kuma ba a halasta siye ko siyar da bayi a wannan zamani da muke ciki, kuma wannan ba ra’ayi na ba ne na son rai. Bincike na ne ya ba ni hakan.

Sa’annan malamai da dama sun tsayu kan irin wannan magana ta waɗannan malamai inda kowanne daga cikinsu ke gabatar da na shi dalillai da hujjoji. Kuma ni dai har zuwa wannan lokacin da nake wannan rubutu ban ci karo da wani bayani da wani sanannen malami ya yi da zai gamsar kan cewa akwai bayi a yanzu kuma da inda ake samun su. Sai dai ba Ina nufin babu malaman da suka tabbatar da wanzuwar bayi a yanzu ba, sai dai ni ban tava ji ba.

Abinda nake so ki fahimta a nan shi ne, tsakanin ƙasashen Afrika ko na ce mu nan da kuma maƙwabtanmu dukkanmu an haramta mana bauta da kuma bautar da mutane a matsayin bayi a hukumance kenan, kuma an jima ana kame ana kuma ‘yanta waɗanda aka qi ‘yantawa, tare kuma da hukunta su masu, dalilin qin jin maganar gwmnati. Kuma har zuwa yanzu wannan dokar a haka take.

Idan kuwa haka ne, ba a yaƙi wanda Musulunci ya halasta a yi, sannan a samu halastattun bayi, wani kaso na bayin an kilacce su a matsayin kuyangu, sannan gwamnati ta ƙwace kaso mai yawa na bayin ta ‘yanta su, menene zai rage na daga bayin? Ko akwai su inaga ba wani tasiri suke da shi ba, kuma zai iya yiwa su zama tarihi cikin ƙanƙanin lokaci, kasantuwar ba su ƙaruwa sai dai raguwa.

Akwai abinda ake kira da ‘ijtima’in malamai’, wato haɗuwa kan matsaya guda dangane da wani sha’ani na Musulunci da ya hudo kai, wanda bai da hukunci kai tsaye a cikin littafi mai tsarki, ko manzon rahma bai magantu kansa ba, sakamakon zamani ko wasu dalilai, hakan ba yana nufin babu zancen da zai iya warware shi ba, kasancewar Allah SWT Shi ne zamanin gabakiɗaya, sai dai yana a dunƙule, kuma malamai waɗanda Annabin Allah ya tabbatar su ne magada annabawa, za su zauna, su yi bincike mai zurfi a tsakanin littafi mai tsarki da kuma maganganun manzon Allah, su samo wani abu da ke kamaiceceniya da shi, ko wani bayani da ya zama saqo ga ‘yan baya, wato maganganun yadda za a iya warware wasu mas’aloli idan sun taso. Da ire-iren waɗannan ne malamai za su kafa hujja su bayar da abinda suka ga ya fi dacewa da hukuncin abinda ake son nemowa.

To a wannan ne za a yi amfani da mafi rinjaye daga cikinsu, wato inda kaso mai yawa daga cikinsu suka dosa, suke ganin shi ne daidai. Wannan ne abinda Musulunci ya aminta da shi game da matsalolin da suka shafi canjin lokaci.

Ko wannan kawai muka yi duba da shi, za mu iya cewa, matuqar malamai za su iya bincike mai tsayi su samo ƙwararran hujjojin da za su tabbatar da wanzuwa ko shuɗewar bayi, to ya halasta mu bi su, kuma mu tsayu kan samuwa ko rashin samuwar su.

Idan mun koma kan ke karan kanki da ki ke kan wannan tafarki, zan so ki fara da tambayar kanki shin wane ne mahaifinki? Shin shi ma kamar mahaifiyar yake ƙarƙashin mutumin da suka kawo ki ko wani irinsa? Waɗanne alamomi ne ke tare da shi da za su iya nuna alamar ba shi da ikon kansa sai na wani?

Gava ta biyu ita ce, yiwan ba ki san mahaifinki ba, an tava nuna maki wani da sunan shi ne ya yi sanadin zuwanki duniya? Kuma ya yanayin kamaninki da waɗanda ku ke tare da su suke?

Za mu ci gaba.

By Editor