Cece-kuce ba zai canja hukunce-hukuncenmu ba – Alƙalai

Daga BASHIR ISAH

Babban Alƙalin Najeriya (CJN), Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya jaddada cewa cece-kucen da ake yi a ƙasa ba zai canja hukunce-hukuncensu kan shari’un siyasa ba.

Kawo yanzu, hukunce-hukuncen da Kotun Ƙoli ta yanke kan batutuwan zaɓe, wanda hakan ya yi sanadiyar soke nasarar wasu gwamnoni da ‘yan majalisu, ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan ƙasa musamman ‘yan siyasa.

Da yake jawabi a wajen buɗe zama na musamman na fannin shari’a na 2023/2024 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyin Nijeriya su 58, Ariwoola ya buƙaci alƙalai da su yi tsayin daka game da ayyukansu.

Ya ce, “Ina buƙatar kowane jami’i a ɓangare shari’a ya zage dantse ya yi aiki tuƙuru da kwatanta gaskiya tare da sauke nauyin da ya rataya a kan kowa bil hakki.

“Sannan ku sani cewa, son kai ko makamacin haka ba zai taɓa maye gurbin doka ba wajen yanke hukuncin duk wata shari’a da ke gabanku.

“Doka sunanta doka, kuma ko a kan wane ne. Don haka a matsayinmu na masu fashin baƙi kan doka, mu zamo masu kauce wa bin ra’ayi da zato sannan mu riƙe gaskiya.

“Kada mu taɓa bari cece-kucen masu magana ya karkatar mana da hankalinmu har ya kai ga muna yanke hukunci saɓanin doka,” in ji shi.

Haka nan, ya ce daga watan Disamban 2022 zuwa Yulin 2023, Kotun Ƙoli ta karɓi kes guda 1,271, kuma daga cikin wannan adadin, Kotun ta saurari shari’u da suka shafi siyasa guda 388.

CJN ya kuma ta ɓotun ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen kyautata fannin shari’a da ma walwalar ɗaukacin ma’aikatan fannin.