Sai an tallafa wa ƙananan masana’antu idan ana son karya farashin shinkafar gida – Ambasada Ali

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Ambasada Alhaji Ali Idris Mai Unguwa Kura, Shugaban Ƙungiyar Masu Sarrafa Shinkafa, Sayarwa da Noma ta na Ƙaramar Hukumar Kura, kuma Shugaban Ƙungiyar Masu Ƙananan Masana’antu da Matsakaita na Sarrafa Shinkafa na Ƙasa, reshan Jihar Kano, ya bayyana cewa ƙorafi da koke-koke da ake yi na tsadar shinkafa, wannan ya samo asali ne daga ƙarancin masu sarafa ta.

Alhaji Ali ya ƙara da cewa, “idan har ana son noma shinkafa ya bunƙasa cikin tsafta, ya kuma wadata, da babu tsakuwa ko ƙuƙus, a cikin ta cikin farashi mai sauƙi da rahusa, sai an tallafawa ƙanana kamfanoni shinkafa, da matsakaita ta hanyar ƙungiyar mu ta ƙasa wacce ke ƙarƙashin jagorancin Alhaji Idris Isa Funtuwa Ɗan Ruwatan Hausa, shugaban wannan ƙungiya na ƙasa wanda koyaushe yana can tare da manya don samo wannan tallafin daga gwamnati.”

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban Ƙungiyar Masu ƙananan Masana’antu da Matsakaita na Ƙasa reshen Jihar kano Ambasada Ali Idris Mai unguwa a Ganawar sa da manema labarai a ranar Juma’ar da ta gabata.

Haka kuma ya cigaba da cewa, idan aka lura manyan kamfanoni da gwamnati tarayya take basu tallafi mai tsoka, na biliyoyin nairori amma farashin shinkafar sai tashi yake koda yaushe, wannan ya nuna gazawar manyan kamfanonin Nijiriya wajen saukar da farashin shinkafa, to tun da haka ne mu a gwadamu a gani, yadda zamu karyar da farashin shinkafa wanwaras a ƙasa in dai gwamnati ta bamu haɗin kai da tallafi na samar da injina masu sarafa shinkafa da rege tsakuwa, ta hanyar da gwamnati ta san tana bawa masana’antu tallafi ga ahalin abun na gaskiya ba masu ci da gumun masana’antu ko manoma ba da sauran su, kasancewar masu sarafa shinkafa da manoma karma jini da hanta ne basa rabuwa domin sai da manomi masana antu zasu rayu, to suma suna da buƙatar tallafin kayan aiki na zamani kamar irin su motocin ko taractocin noma da taki da iri na zamani da magungunan kwari da sauransu cikin sauqi wannan zai taimaka wajen samar dawadar ciyar shinkafa da kayan abinci wanda zai karya farashin kayan abinci.

Hakazalika, Ambasada Ali Idris Mai Unguwa ya ce, a yanzu haka da mu ke kakar shinkafa muga farashin ta ya karye idan akayi la akari da cewa kafin wannan lokaci ana sai da kwanan shinkafa ko Mudu mai gwangwani shashida akan Naira 1600 ko da 1700 zuwa 2000 kololuwar mai kyau inda kafin wannan lokaci ƙololuwar mai kyau na iya kai ya 2300 koma sama da haka amma yanzu ga yadda take wanda a baya buhun samfarera na kai 36000 ya ko daga 25000 ne zuwa 30000 qololuwarsa ya danganta yaje sayo kaya da kuɗin sufuri, kuma wani abun farin ciki du wannan hawa da sauka na farashin shinkafa har yanzu ba a taɓa cewa shinkafa ko abinci ya yanke a Nijiriya ba har a zamanin Korona,sabo da Allah ya albarkaci da samun abinci saɓanin wasu ƙasashen duniya.

A qarshe ya ce, manoman Nijiriya na da ƙoƙari musamman idan aka dubi yadda manoman Kano, Kebbi, Taraba, Adamawa da sauransu ke samar da shinkafa wannan buƙatar kulawa ne ta musanman da gwamnatocin mu za su yi na inganta Noma, wanda ko mu anan yankin Kura da Madobi muna noma hekta samada dubu 22 wacece hekta ɗaya akan samu buhu 70 zuwa 80 ya danganta da gyaran gona da albarka ƙasa inda kuma ya buqaci ‘yan jarida da su riƙa binci ko farshin mafi sauƙi suna bayyanawa ba shaci-faɗi ba kamar yadda wasu kafafan yaɗa labaran ke taimakawa wajan ingiza farashin kaya ta hanyar shaci faɗi.