Gwamnan Kano ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Jihar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar.

Hakan dai na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aiko wa Manhaja,

Inda ya ce naɗin na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar Kano, Usman Bala ya kammala aikinsa, inda ya yi ritaya daga aikin gwamnati tun a watan Mayun shekara ta 2023, kamar yadda doka ta tanada .

Sanarwar ta ce Alhaji Abdullahi Musa ƙwararen ma’aikacin gwamnati ne da ya yi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar Kano, kuma haifaffen Ƙaramar Hukumar Ƙiru ne.

Kazalika, Abdullahi Musa ya taɓa zama Babban Sakatare a Gidan Gwamnatin Jihar Kano da majalisar zartarwa ta jihar da kuma ma’aikatar ayyuka na musamman da dai sauransu.

Sannan Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da ya gudanar da aikin sa cikin ƙwarewa da bin dokoki da ƙa’idojin aikin gwamnati.